Abin da Magu ya fada mani da Shugaba Buhari ya nada ni Inji sabon Shugaban EFCC


Sabon shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa, Mista Abdulrasheed Bawa, ya yi magana a kan alakarsa da Ibrahim Magu. Jaridar legit ta ruwaito.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Abdulrasheed Bawa ya na cewa akwai dangantaka ta mutunci tsakaninsa da tsohon mukaddashin shugaban EFCC, Ibrahim Magu.

Abdulrasheed Bawa ya bayyana haka ne yayin Sanatoci su ka tasa shi a gaba, su na yi masa tambayoyi domin a tantance shi a matsayin sabon shugaban EFCC.

Da yake jawabi yau, Abdulrasheed Bawa ya bayyana yadda Magu ya kira shi a waya, ya taya shi murna a lokacin da aka zabe shi a matsayin sabon shugaban hukumar.

“Ina da alaka mai kyau da tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC. Ya kira ni da aka zabe ni, ya yi mani fatan Ubangiji ya ba ni sa’a.” inji Abdulrasheed Bawa.

Jaridar ta ce Sanatocin sun yi wa Bawa tambayoyi a game da yadda ‘yan jarida su ke ruruta labaran ‘yan siyasar da ake bincike da zargin satar kudin al’umma.

Har ila yau, Bawa ya ce EFCC sun yi nasara a fiye da 90% na karar da ta shigar a kotu. Bawa yake cewa EFCC ta yi nasarar daure ‘yan damfara duk da yawan bata lokaci.

Bawa ya yi aiki a karkashin Magu wanda ya kasance mai gidansa a EFCC tsakanin 2016 da 2020. Har ana rade-radin an taba samun sa da aikata ba daidai ba a lokacin.

A tsakiyar shekarar bara ne aka dakatar da Ibrahim Magu daga aiki, sannan aka kuma nada wani kwamiti na musamman da ya yi bincike a kan ayyukan da ya yi a EFCC.

A yau, 24 ga watan Fubrairu, 2021, Mista Abdulrasheed Bawa, ya bayyana a gaban ‘yan majalisa. Kamar yadda ku ka ji, Sanatoci sun tabbatar da Bawa bayan tantacewar.

Bayan wani 'dan lokaci majalisar dattawan ta amince da AbdulRasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar hana almundahana da yi wa tattalin arziki zagon-kasa.

Shugaban majalisa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya sanar da hakan a zauren majalisar.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN