AbdulRasheed Bawa: Abubuwa biyar da ya kamata ku sani kan sabon shugaban EFCC


Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da AbdulRasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasar ta'annati.

Idan majalisar dattijan Najeriya ta amince da shi, ɗan asalin jihar Kebbi a Najeriya AbdulRasheed Bawa zai zama shugaban hukumar na biyar bayan Nuhu Ribadu da Farida Waziri da Ibrahim Lamorde da Ibrahim Magu.

Haka kuma, na farko daga yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Ga wasu abubuwa biyar dangane da sabon shugaban na EFCC da watakila ba ku sani ba.

1. Shi ne mafi karancin shekaru cikin duka shugabannin hukumar

AbdulRasheed Bawa shi ne mafi ƙarancin shekaru cikin duka shugabannin hukumar EFCC idan majalisar dattijan Najeriya ta amince da naɗin nasa.

Shugaban Hukumar na farko, Malam Nuhu Ribadu ya hau muƙamin ne yana da shekaru 43 yayin da Lamorde ya hau yana da shekaru 49.

Ita kuwa Farida Waziri ta hau muƙamin ne tana da shekaru 59.

Ibrahim Magu ya zama shugaban EFCC yana da shekaru 53.

2. Shi ne shugaban hukumar na farko da ba ɗan sanda ba

Duka tsoffin shugabannin hukumar EFCC sun kasance tsoffin ma'aikatan rundunar ƴan sandan Najeriya.

AbdulRasheed Bawa shi ne shugaban hukumar na farko da ba ɗan sanda ba kuma ya kasance asalin ma'aikacin EFCC ne.

Yana cikin ma'aikatan farko na hukumar da aka ɗauka aiki a shekarar 2004 kuma bai taɓa aiki a ko ina ba sai a EFCC.

3. Ya jagoranci binciken da hukumar ke yi kan tsohuwar Ministar Man fetur Diezani Alison-Madueke

A shekarar 2015 ne aka naɗa AbdulRasheed Bawa shugaban kwamitin bincike na hukumar kan Diezani Alison-Madueke, tsohuwar Ministar Man fetur ta Najeriya.

Tawagarsa ta gano gidaje da kuɗinsu ya kai miliyoyin dala a Najeriya da Burtaniya da Amurka da Haɗaɗdiyar Daular Larabawa.

Baya ga binciken Diezani, Bawa ya jagoranci bincike da dama da shari'o'in da aka yi nasarar kama masu laifin da gano ƙudi da dukiyoyin da aka sace a fadin duniya.

Haka kuma, yana cikin waɗanda suka gudanar da binciken almundahanar cire tallafin man fetur da aka yi a Najeriya tsakanin shekarun 2012 zuwa 2015

4. Ya yi karatu a Jami'ar Usmanu Ɗanfodio, Sakkwato

AbdulRasheed Bawa ya yi digirinsa na farko a fannin Tattalin Arziki kuma ya kammala a shekarar 2001.

Sannan ya yi digirinsa na biyu a ɓangaren Diflomasiyya inda ya kammala a 2012 duk Jami'ar Usmanu Ɗanfodio da ke Sakkwato.

Wasu rahotanni sun nuna cewa a halin yanzu yana karatun aikin shari'a a Jami'ar Landan.

5. Ya yi aiki ƙarƙashin duka tsoffin shugabannin na EFCC

AbdulRasheed Bawa ya yi aiki da duka shugabannin hukumar na baya.

A zamanin Nuhu Ribadu ya fara aiki a hukumar a shekarar 2004, kuma bayan aiki a ofishin EFCC na Legas na wani lokaci ya dawo hedikwata da ke Abuja inda ya yi aiki tsawon lokaci.

Yana cikin ƙananan jami'ai da aka ƙaddamar na farko a shekarar 2005.

Daga nan kuma ƙarƙashin duka shugabannin na baya, Bawa ya haye matakai da dama har ya kai matsayin Deputy Chief Detective Superindent (DCDS), matsayin da yake ri ƙe da shi tun shekarar 2016 har ya zuwa yanzu da Shugaba Buhari ya zaɓe shi a matsayin sabon shugaban EFCC.

Rahotun BBCHausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN