Yanzu Yanzu: Rundunar yan sanda ta sake rashin AIG na biyu cikin kwanaki 3


Mataimakin babban sufeton rundunar yan sandan Najeriya, Yunana Babas ya rasu. Shine ke kula da Zone 8, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ya rasu kwanaki uku bayan mutuwar wani mataimakin babban sufeton yan sanda, Omololu Bishi.

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrazaq Abdulrahman, ya yi ta’aziyya ga hukumomin yan sanda a kan rashin da suka yi.

Abdulrahman ya bayyana Babas a matsayin kamilin mutum kuma jajirtaccen jami’i.

“Na samu labarin mutuwar AIG Yunana Babas cikin dimuwa da bakin ciki.

“A madadin mutane da gwamnatin jihar Kwara, ina ta’aziyya ga dukka ahlin dan sandan, musamman Sufeto Janar na yan sanda da iyalan babban jami’in.

“Marigayin ya kasance kamilin mutum, wanda ya taimaka wa kasa, kuma kwararren dan sanda wanda ke yiwa kasarsa hidima. Na tuna da rawar ganin da marigayin ya taka a wasu lamuran tsaro a yankin."

Gwamnan ya yi wa marigayin addu’an samun jin kai a wajen Allah da kuma ba iyalansa dangana.

A wani labarin, Sultan na Sokoto, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya rasa kaninsa, Abdulkadir Jeli Abubakar III.

PM News ta ruwaito cewa Jeli ya mutu a ranar Alhamis, 14 ga watan Janairu yana da shekaru 64 a duniya.

Legit.ng ta tattaro cewa Jeli, wanda ya kasance kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Sokoto, ya mutu bayan yayi fama da rashin lafiya.

Mai ba Gwamna Tambuwal shawara a kan labarai, Malam Muhammad Bello, ne ya tabbatar da mummunan labarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN