Rikici ya barke yanzu haka a daki na 028, inda aka shirya taron tattaunawa da jama'a kan dokar kamfanin man fetur PIB tsakanin wasu suka halarci zaman.

Rahoton Vanguard ya bayyana cewa har yanzu ba'a gane wadanda suka tada rikicin ba amma ana kyautata zaton wasu yan jihohin Neja Delta ne.

Rikicin ya barke misalin karfe 12:10 na ranar lokacin da shugaban kwamitin, Hanarabul Mohammed Munguno, yayi kira ga yan jihohin Neja Deltan su gabatar da jawabinsu.

Kawo yanzu, yan majalisa da sauran wadanda ke hallare a wajen su gudu daga dakin.

Karin bayani na nan tafe.


Source: Legit Newspaper