Yanzu yanzu: Kotu to tona wa APC asiri, ta yi watsi da kara kan Obasaki na PDP


Wata babbar kotun tarayya dake zaune a Abuja ta yi watsi da karar amfani da kwalin jabu da jami'yyar All Progressives Congress APC ta shigar kan gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Alkali Ahmed Mohammed ya yi watsi da karar nan ranar Asabar, Channels TV ta ruwaito.

APC da wani jigon APC Edobor, sun shigar da karan cewa gwamna Obaseki ya yi amfani da takardan bogi yayinda yake neman takaran gwamnan jihar da akayi ranar 19 ga Satumba, 2020.

A hukuncin da ya yanke, Alkali Mohammed yace APC sun dogara da kwafin da Obaseki ya gabatarwa INEC ba tare tuntubar jami'ar don sanin sihhancin kwalin ba.

Ya kara da cewa babu gaskiya cikin karar da APC ta shigar.

Alkalin ya kara da cewa mataimakin rajisran jami'ar Ibadan ya gabatar da hujjan cewa lallai Obaseki yayi karatu a jami'ar kuma sun bashi kwali.

Gwamna Obaseki ya samu nasara a zaben gwamnan jihar Edo da ya gudana ranar 19 ga Satumba, 2020.

Obaseki ya lallasa Ize-Iyamu da kuri'u sama da 80,000 kamar yadda hukumar INEC ta sanar:


yadda hukumar INEC ta sanar:

Masu zabe da aka tantance: 557,443

PDP: 307,955

APC: 223,619

Bayan zaben, jam'iyyar APC ta bayyana cewa ba zata kalubalanci sakamakon zaben a kotu ba amma za ta cigaba da tuhumar gwamnan da amfani da takardun bogi


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN