Wata mahaifiya tare da Jaririn da take goye da shi a cikin Keke napep sun mutu bayan motar Hilux na yansanda ta ci karo da Keke napep da suke ciki sakamakon haka matar da jaririnta suka mutu nan take a Birnin Warri na jihar Delta.
Shafin ISYAKU.COM ya samo cewa ana zargin cewa wasu yansandan ofishin yansanda na Ebrumede ne suka biyo wasu samari a guje da motarsu kirar Hilux da niyyar kamasu bayan sun yi zargin cewa yaran yan Yahoo ne.
Garin tsananin gudu don ganin sun kama samarin, sai motar Hilux da yansandan ke ciki ta ci karo da Keke napep da matar ke ciki goye da jaririnta, lamari da ya sa Keke napep ya ruguje kuma matar da jaririnta suka mutu nan take.
Ganin haka ke da wuya,, sai yansanda suka yi kokarin tserewa, amma matasa suka hana su zuwa ko ina, kuma suka banka wa motar yansanda wuta ta kone kurmus.
Sai dai kawo yanzu ba wani bayani kan ko me ya faru da yansandan.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari