Yadda uwargida ta kashe budurwar mijinta a Kano kwana 3 kafin daurin


Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wata matar aure mai shekaru 20 mai suna Suwaiba Shuaibu a kan zarginta da sokawa wata Aisha Kabir wuka ana sauran kwanaki kadan aurenta.

An gano cewa Aisha ce wacce Malam Shahrehu Alhaji Ali, mijin wacce ake zargin zai aura a ranar 9 ga watan Janairu a kauyen Gimawa, karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano, Daily Trust ta wallafa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Talata, ya ce an nema amaryar an rasa amma daga baya sai aka ga gawarta a wani kango.

Kamar yadda takardar tace: "A ranar 2 ga watan Janairu wurin karfe 10:30 na safe mun samu labarain ganin gawar Aisha Kabir daga kauyen Gimawa a wani kango.

"Mai korafin ya ce ana zargin an soka mata wuka ne a wuya. Mun ziyarci wurin inda muka dauka gawarta zuwa babban asibitin Tudun Wada wanda likita ya dubata.

"Kwamishinan 'yan sanda CP Habu A. Sani ya bukaci jami'an tsaro da su nemo wadanda suka yi aika-aikar.

"A wannan halin ne aka damko Suwaiba Shuaibu mai shekaru 20. Bincike ya nuna cewa mijinta ya kashe shekaru 6 suna soyayya da budurwar kuma za su yi aure."

Kiyawa ya ce wacce ake zargin ta amsa laifinta. Ta ce da kanta ta kira budurwar mijinta sannan ta kaita kangon ta soka mata wuka a wuya, kirji da sauran sassan jikinta.

Ya ce an mika lamarin hannun sashin bincike na musamman kan kisan kai kuma za a mika wacce ake zargin a gaban kotu.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Lahadi ya gabatar da motocin alfarma biyu ga sabon Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin Elkanemi domin saukaka masa tafiye-tafiye da al'amuran mulkinsa.

Daya daga cikin motocin akwai kirar SUV Lexus ta 2020 sai wata kirar Toyota Hilux ta 2020.

Babban sakatare a ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu, Tarfaya Asariya, wanda ya samu rakiyar kwamishinan ayyukan noma, Injiniya Bukar Talba ne suka mika motocin.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN