Yadda sabon bidiyon sabuwar wakar Hausa ya fusata Hausawa


Sakin wani faifan bidiyon sabuwar wakar Hausa a shafin YouTube da sauran dandalin sada zumunta ya fusata Hausawa tare da yin tofi Alla-wadai da da wakar, wacce suka ce ta sabawa al'ada Bahaushe.

Wadanda suka soki sabuwar wakar, mai suna 'North Vibe' wacce mawaki Abdullahi Aliyu Shelleng ya rera kuma ya wallafa, sun yi korafin cewa an nuna tsiraici a faifan bidiyon wakar.

Jaridr Daily Trust ta rawaito cewa mawakin, wanda aka fi sani da AA Shelleng, haifaffen jihar Adamawa ne kuma ya nadi faifan bidiyon sabuwar wakar tare da wani mawaki mazaunin Legas mai suna SlimCase.

Sabuwar wakar ta fusata Hausawa a dandalin sada zumunta lamarin da yasa suka yi rubdugun wajen yin martani tare da zargin cewa faifan bidiyon wakar ya ci mutuncin yare da al'adun Hausa.

Wani mai suna Tajuddeen Musbahu ya mayar da martani kamar haka; "wannan ya sabawa al'adu da tarbiyar arewa. Wannan tamkar cin mutunci ne ga duk mutanen da ke yaren Hausa, ina mai bayar da shawarar a goge wannan faifan bidiyo daga yanar gizo domin bai kamata ba, kuskure ne."

Wani mutum ya sake bayyana nasa ra'ayin kamar haka; "na tabbata wannan gayen ba dan arewa bane, babu yadda za'a yi Bahaushe ya yi haka ba tare da an samu mai tsawatar masa ba. A takaice, babu wata kabila a Nigeria da zata so a alakanta ta da wannan faifan bidiyo.

"Ya kamata hukuma ta dauki mataki a kan wannan yunkuri na son cin mutunci da zubar da kimar wani yare ba tare da wani dalili ba.

A ranar Litinin, 11 ga watan Janairu, Legit.ng ta rawaito cewa Jarumar Kannywood, Rahama sadau, na fuskantar sabuwar caccaka daga masoyanta Musulumai sakamakon bayyana bangaren jikinta

Mabiyan jarumar sun mayar mata da martani kan hoton da ta ɗauka da jarumar masana'antar Bollywood, Shabnam Surayyo

Sai dai jarumar ta dawo shafinta na Tuwita ta wallafa wata maganar da Priyanka Chopra ta taba yi akan jajiracewa yayin suka da tsangwama.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN