Yadda ake amfani da rake don kare tamukewar fatar jiki,tsufa,mura da zazzabi


Wata kwararrar masaniya kan ilimin lafiyar tu'ammali da kayakin abinci mai suna Mrs Olufunmilola Adewumi, kuma mataimakiyar shugaban sashen kula da lafiyar kayakin abinci na al'umma a Asibitin General Hospital da ke Agege a jihar Lagos ta ce shan Rake yana taimakawa jikin dan Adam wajen yaki da kwayoyin cuta.

A cewar Adewumi, sinadarin ruwan rake baya dauke da mai, kitse, protein ko sodium.

Ta ce rake na dauke da sinadarin vitamin C, vitamin B2, magnesium, iron, potassium da phosphorus.

Ta kara da cewa rake na taimakawa wajen hana bushewar fatar jiki, yana taimakawa wajen rage kiba, inganta aikin kayan cikin Dan Adam, taimakawa wajen narke abinci a cikin Dan Adam, ba  da kariya ga cututtuka a jikin Dan Adam,  bayar da kariya ga zazzabi.ko masassara da kuma magance wasu nau'in sanyi da mura.

Ta ce sinadarin alkaline da ke cikin ruwan rake yana taimakawa wajen kare matsalar hauhawan sinadarin jikin Dan Adam watau hyperacidity, tare da taimakawa wajen rage zafin ciki da zafi da kuna a zuciya, tare da kare jiki daga kamuwa da cutar daji, ko Sankara watau cancer.

Yana taimakawa wajen kare kaikayin jikin Dan Adam, ruwan rake asalin sinadarin Alpha Hydroxide Acid ne, wanda ya hada da sinadarin glycolic acid wani sinadari da ake amfani da shi domin hana tamukewat fatar Dan Adam don tsufa a cikin man shafawa 

Kazalika ruwan rake matukar an sha kan ka ida, yana daidaita aikin Koda kamar yadda ya kamata,  ta haka zai iya zama kariya ga cutar Koda da matsalolin kafar mafitsara .

Ta ce matukar an sha rake daidai yadda ya kamata ba tare da zarce kaida ba, rake bai da illa ga masu cutar suga watau Diabetes,  domin shan rake daidai wa daida baya haddasa hauhawan yawan suga a jinin biladama" a cewar Adewumi.

Rahutun Isyaku Garba Zuru.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN