Wata Kotu ta daure wata gawa a Kurkuku tare da cinta tara N50,000

SHARI'A SAƁANIN HANKALI WATA KOTU A A KANO TANA SHIRIN ƊAURE WATA GAWA DAKUMA CINTA TARA HAR 50,000


Kotun a Kano ta ci tarar gawa Naira 50,000 ko daurin shekara daya Kotun majistary mai lamba 44 da ke zamanta a gidan Murtala da ke Kano, ta yankewa wani mutum mai suna Abubakar Bello da tuni da aka ce ya mutu daurin shekara guda a gidan yari. Mai shari’a Rakiya Lami Saleh ce ta yanke hukunci.

Tun da fari dai an gurfanar da Abubakar Bello a gaban kotun bisa laifin satar mota. To amma ana tsaka da shari’ar ne aka gabatarwa da kotu takardu na cewar wanda ake tuhuma fa ya mutu.Hakan ya sa mai shari’a ta rufe shari’ar tunda ba a shari’a da gawa.

To sai dai bayan rufe shari’ar ne kwazam sai aka hango wanda aka ce ya mutun yana yawo gari. Hakan ce ta sanya aka yi masa tarko da wata zulakekiyar budurwa, aka kuma sake kamashi. Ɗan sandan kotu mai gabatar da kara ASP Ahmad Mukhtar ne ya sake gurfanar da shi gaban kotun bisa zarginsa da laifin satar mota da ake yi masa tun a baya. Haka kuma mai shari’ar bayan nazari da bincike ta tabbatar da laifin da ake zarginsa da shi.

Mai shari’a Rakiya Lami Saleh ta yankewa Abubakar Bello daurin shekara guda a gidan yari, ko kuma zabin tarar N50,000 

Daka Alhaji Sani Sani Maigatari


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN