Tantabarun da Buhari ya saki a bikin ranar tunawa da Sojoji sun ki tashi (Bidiyo)


Fararen tantabarun da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya saki a bikin ranar tunawa da jaruman Sojojin Najeriya sun ki tashi duk da yunkurin da shugaban kasan yayi.

Hakan ya janyo cece-kuce a kafafen ra'ayi da sada zumunta ranar Juma'a, 15 ga Junairu, 2021.

Sakin tantabarun wani al'ada ne da aka saba yi domin nuna cewa Najeriya na cikin zaman lafiya da lumana da kuma soyayyar juna.

Mai jagorantar bikin ya bayyana hakan yayinda shugaba Buhari ke kokarin ganin tantabarun sun tashi amma suka kiya.

Buhari ya bude kejin, ya dauki daya daga cikin tantabarun, ya jefa sama amma tantabarar ta dawo kuma taki tashi.

Bayan haka, Buhari ya bude kejin gaba daya domin dukkan tantabarun su tashi amma sukayi zamansu ciki yayinda wasu suka zauna a kan murfin kejin.

Shugaban kasan da ya gaji, sai ya hakura ta bar tantabarun kuma ya koma kujerarsa. Amma bayan wani lokaci da Buhari ya tafi, wasu cikin tantabarun suka tashi.

Bincike ya nuna cewa tantabarun gida irin wadannan basu fiye damuwa da tashi ba.

Fafaroma Francis ya bada umurnin daina wannan al'ada a 2014 yayinda tantabaru biyu suka ki tashi a wani taro.

Hakazalika a 2014, tantabarun sun ki tashi lokacin da shugaba Goodluck Jonathan ya sake su.

Babban faston Adoration Ministry, Fada Mbaka, a lokacin yace wannan alama ce dake nuna Allah ba ya bayan Jonathan.

Yanzu haka mutane na tofa albarkatun yawunsu kan lamarin da ya auku yau Juma'a.

Ganewa kan ka bidiyon:

A bangare guda, shugabannin Najeriya fari daga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zuwa kasa sun halarci bikin ranar tunawa da jaruman Sojojin Najeriya da aka saba duk shekara.

Kamar yadda aka saba, an gudanar a bikin bana ne a farfajiyar Eagle Square dake kwaryar birnin tarayya Abuja.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila; da shugaba Alkalan Najeriya, Justice Muhammad Tanko

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN