Kotu ta jefa direba Kurkuku kan kashe N2m da aka tura masa cikin kuskure


Wata kotu dake zaune a Ilori, birnin jihar Kwara, ya yankewa wani direba hukuncin shekaru biyu a gidan kaso kan amfani da kudin da ba nashi ba.

Direban, mai suna Adetunji Tunde Oluwasegun, ya yi amfani da kudi milyan biyu da wata mata Sherrifat Omolara Sanni ta tura asusun bakinsa na GTB cikin kuskure.

Ofishin hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da shi a kotun ranar Litinin, 18 ga Junairu, 2021.

EFCC ta gurfanar da direban gaban Alkali Sikiru Oyinloye na babban kotun jihar Kwara kan laifin sata.

A cewarsa, laifin ya saba dokar sashe na 286 da 287 na PenalCode.

Alkali Sikiru Oyinloye ya kama direban da laifin aikata sata kuma ya yanke masa hukuncin shekaru biyu a gidan kaso tare da biyan kudin tara N200,000 (Dubu dari buyu), EFCC ta bayyana.

Bugu da kari, kotu ta umurci direban ya mayarwa matar da kudin milyan biyu cikin shekaru biyun da zai yi a gidan yari.

A bangare guda, ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa akan Naira miliyan dari tara (N900,000,000) gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar samar da shafin yanar gizo domin sayen tikitin jirgin kasa.

Amaechi ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin bikin kaddamar da shafin wanda zai koma hannun hukumar kula da jiragen kasa bayan shekara goma.

A cewar ministan, an damka kula da gudanar da shafin yanar gizon a hannun wani kamfani kafin daga bisani ya mayar da shafin hannun hukumar NRC.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN