Gwamnan arewa ya tona asirin inda aka dauko yan bindiga da ke addaban arewa


Gwamnan Jihar Niger Abubakar Sani-Bello, a ranar Laraba, ya ce 'yan bindiga daga kasashen Mali da Sudan suna kai hare-hare a wasu yankunan Arewa, The Nation ta ruwaito.

A cewarsa, yan bindigan sun shigo kasar ne a kan babura kuma a dandalin sada zumunta ake nemansu - musamman Facebook.

Gwamnan na Jihar Niger, wadda ya bayyana hakan a ranar Laraba, ya ce ya mika batun da wasu kallubalen tsaro da jiharsa ke fuskanta ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya yi magana da manema labarai a gidan gwamnati bayan ganawarsa da shugaban kasa.

Niger na daya daga cikin jihohin Arewa da ke fama da kallubalen 'yan bindiga.

Sani-Bello ya kara da cewa wasu yan bindiga daga jihohin Zamfara da Kaduna suna kai hare-hare jiharsa.

Ya kara cewa, baya ga matsalar yan bindiga da wasu laifuka, batun rashin abinci, kona daji da kashe dabobi na cikin abubuwan da ke addabar jihar.

Gwamnan ya yi bayanin cewa ya ziyarci Shugaba Buhari ne domin neman tallafin gwamnatin tarayya kan batun yan bindiga da gyaran tituna da suka lalace a jiharsa.

Wani sashi cikin jawabin gwamnan "Matsalar babba ne. Neja na da girman kilomita 73,000. Girman Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas kenan (Idan an gwamutsa su). Da farko, muna da karancin jami'an tsaro kuma ina ganin ya kamata mu kara adadinsu da za su yi aiki a dukkan sassan jihar.

"Muna samun yan bindiga suna shigowa daga jihohin da ke makwataka da mu musamman Zamfara da Kaduna. Yana da wahala a tsare dazukan don motoccin mu ba zasu iya shiga dajin ba, don haka muna taimakon gwamnatin tarayya musamman sojojin sama. Sojojin saman na bada taimako sosai kuma suna samun nasarori."

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN