Gwamna Tambuwal ya sauke shugabannin kananan hukumomin Sokoto, duba dalili


Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya rushe kafatanin shugabannin kantomomin riƙo na ƙananun hukumomi 23 dake faɗin jihar.

Gwamnan ya rushe kwamitin ne ran juma'a da ta gabata jim kaɗan da ganawarsa da su a gidan gwamnatin jihar ta Sokoto.

Ya bayyana gamsuwarsa bisa goyon baya da kwarin gwiwa da suka baiwa gwmanatinsa inda ya bayyana cewa "Duk kun yi iya ƙoƙarin ku don tabbatar da nasarar wannan gwamnati shekaru biyu baya da kuma bayan zaɓe."

"Duk kun san cewa ka'ida ta tsawon zangon mulkin ku shine wata shida, amma zuwa yanzu shekaru biyu kan karagar mulki,' in ji gwamnan.


"Ina sane da wasun ku za su nemi tsayawa takara. Ina yi musu fatan alheri. Ko kun dawo ko ba ku dawo ba, za mu cigaba da tuntubar juna duk sanda buƙatar hakan ta taso."

Cikin bayanin sa, tsohon shugaban ƙaramar hukumar gudanarwa ta Sokoto ta Arewa, Alhaji Aminu Ibrahim, da aka fi sani da No Delay, a madadin sauran takwararorinsa, bayyana godiya ya yi ga gwamnan bisa dama da ya ba su na yiwa jama'ar yankunansu aiki.

"Za mu cigaba da mara maka baya saboda mun fahimci manufarka ta son cigaban al'ummar jihar nan ne." In ji No Delay.

Legit.ng ta rawaito cewa Nasir El-Rufa'i, gwamnan Kaduna, ya sauke sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jihar 23 watan Disamba, 2020.

Kazalika, gwamnan ya sauke shugaban hukumar CSDA tare da maye gurbinsa da Sauda Amina-Ayotebi

Gwamnan ya ce an yi sauye-sauyen ne domin inganta aikin gwamnati a jihar Kaduna.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN