Shafin BBCHAUSA ta wallafa cewa Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya Abdullahi Ganduje, ya ce ya kamata a samar da dokar da za ta haramta zirga-zirgar shanu daga arewa zuwa kudancin kasar.
Kafafen yada labarai na kasar sun ruwaito Ganduje na fadin haka a garin Daura da ke Jihar Katsina, lokacin da shi da sauran gwamnonin jam’iyyar APC suka je wurin shugaban kasar Muhammadu Buhari.
Ganduje ya ce matukar ba a dakatar da zirga-zirgar shanu tsakanin yankunan biyu ba, to ba za a taba kawo karshen rikicin manoma da fulani ba.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta samar da wurin kiwo ga masu kiwo a wani daji da ke nusa da iyakar Kano da Katsina.
He said the settlement will have houses, a dam, an artificial insemination centre, and a veterinary clinic.
“Muna gina Ruga a dajin Samsosua da ke kan iyakarmu da Ktsina, kuma munyi nasara wajen shawo kan ‘yan fashin daji a yankin,” in ji Ganduje.
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari