Duba nassarori 19 da Hisbah jihar Kebbi ta samu, na 8 da 9 zasu baka mamaki


A ci gaba da gudanar da ayyukanta wanda ya hada da seta tarbiyyan al'umma, hukumar Hisbah a jihar Kebbi ta yi nassara wajen gudanar da ayyukanta a bangarorin rayuwa da dama a cikin al'umma.

Shafin labarai na ISYAKU.COM ya tattaro bayanai na wasu daga cikin nassarori da hukumar karkashin babban Kwamandan ta na jihar Kebbi Alhaji Sulaiman Muhammad tare da mataimakinsa Alhaji Mamuda Geza da ma'aikatan hukumar Hisbah suka samu na tsawon shekara daya, daga 1/1/2020 zuwa 31/12/2020.

Nassarori da ayyukan Hisbah jihar Kebbi daga 1/1/2020 zuwa 31/12/2020

1-Sulhu tsakanin maza da mata ma'aurata ko tsakanin uba da diyansa= 233
2-Jarirai da aka tsinta=12
3=Yara da ke bacewa a ganesu=93
4-Yara da suka bata ba a ganesu ba har yanzu=30
5-Jan kunne ga maza da mata da hukumar ta yi=69
6-Yi wa yara mata auren Dole=38
7-Mata masu yawon banza ko karuwanci=29
8-Mata masu haihuwa ba aure=26
9-Mata masu cikin banza=35
10-Daura aure da ciki=4
11-Yan mata kanana da ake turowa birni domin yin aikatau a gidaje kuma su fada wani mawuyacin hali ko yanayi=30
12-Yan mata da ake turo wa Hisbah daga wasu jihohi=6
13-Yi wa kananan yan mata fyade=17
14-Yara masu shan tabar wiwi da shisha=28
15-Mata masu matsalar tabin hankali=9
16-Koke kan biyan bashi da Hisbah ta taimaka aka karba=24
17-Matsalar yi wa kananan yara maza Luwadi=4
18-Mutane da suka nemi rabon gado ta hukumar Hisba=2
19-Gawa da basu da gata ba a san su waye ba=2

Alhaji Mamuda Geza , mataimakin Kwamandan Hisbah na jihar Kebbi, ya yi kira ga iyayen yara da ma'aurata su sa ido sosai wajen kula da tarbiyyan ya'ya'nsu a fadin jihar Kebbi gaba daya domin samun al'umma ta gari duba da tarbiyyan na gari na farawa daga gidan iyayen yara.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN