Jaridar Punch ta rahoto cewa ana zargin wannan mutumi mai suna Olaleye Jimoh, da laifin yin lalata da wata Baiwar Allah mai shekaru 50 da haihuwa.
Jami’in ‘yan sanda, Oriyomi Akinwale, ya shaida wa kotu a ranar Alhamis, 28 ga watan Junairu, 2021, cewa ana zargin Mista Olaleye Jimoh da laifin fyade.
Akinwale ya ce an kama matashin ne a ranar 24 ga watan Junairu, 2021, a shiyyar Odo-Owa Ekiti, garin Ikole Ekiti, ana zargin ya aikata laifin ne kafin ranar.
A cewar jami’in tsaron; “Za a hukunta duk wanda ya aikata irin wannan laifi a karkashin sashe na 358 na dokokin laifuffukan jihar Ekiti na shekarar 2012.”
Rahoton ya bayyana cewa Akinwale ya roki kotu ta ba shi damar ya dauki takardar karar ya kai wa darektan tuhuma domin a dauki matakin da ya kamata.
Olaleye Jimoh ya bayyana a gaban kotu, yayin da ya samu wani lauya mai suna, Busuyi Ayorinde, ya tsaya domin ya ba shi kariya daga zargin da ake yi masa.
Alkali mai shari’a, Adefunmike Anoma ta saurari karar, a karshe ta ce a tsare wanda ake zargin.
A ranar 4 ga watan Maris, 2021, mai shari’a Adefunmike Anoma, za ta cigaba da zama domin ta karasa sauraron karar bayan an dakatar da zaman a ranar Alhamis.
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari