Boko Haram sun kwace barikin Sojoji dake Marte, Sojoji sun kwato abinsu


Rundunar jami'an Sojoji da jirgin yaki sun kawar da yan ta'addan ISWAP ada suka kai hari barikin sojoji dake Marte, jihar Borno.

An lalata motocin yaki da makamai yayinda sojojin suka kwace barikinsu da yan Boko Haram suka kwace.

Mutanen dake garin sun gudu daga muhallansu zuwa garin Dikwa.

Yan ta'addan ISWAP sun kai hari, da yammacin Juma'a, barikin Sojoji dake Borno, Arewa maso gabashin Najeriya, HumAngle ta ruwaito.

Rahoton ya nuna cewa har da safiyar Asabar suna cikin barikin.

Bayanan abubuwan da suka auku a harin dai basu bayyana ba har yanzu da ake kawo rahoton.

Wannan hari na zuwa ne lokacin da gwamnatin jihar Borno ke shirin mayar da mutane 300 garin.

A Oktoban 2020, gwamnan jihar ya kaddamar da kwamitoci biyu domin mayar da yan sandanin gudn Hijra Marte, Kirawa da Ngoshe.

Gwamnan na shirin mayar da su wajen ne saboda Marte gari ce na noma da kasuwanci.

Garin Marte ya shahara da noman Alkama.

Gwamnatin jihar a kwanakin baya na tattaunawar samar da wutan lantarki Marte da kewaye domin inganta noman zamani.

Gwamnan na haka ne domin rage adadin mutanen da zama a sansanin yan gudun hijra, hakazalika kuma domin noma, suna da kasuwancin da ke gudana a garin.

A wani labarin kuwa, rundunar Sojin Najeriya sun kashe wasu yan bindiga a harin da aka kai musu a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar.

Aruwan ya ce rundunar mayakan sama sun hallaka yan bindiga da dama kan baburansu a Saulawa, Kuduru da Farin Ruwa.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN