An daure wani mai wa'azi a Turkiyya shekaru 1,000


Wani masanin addinin Islama mai yada shirye-shiryensa a telebijin wanda yake kewaye kansa da mata sanye da kayan badala a talabijin, an daure shi sama da shekaru 1,000 a ranar Litinin saboda aikata laifuka na lalata, in ji kafofin watsa labarai na cikin gida, Channels Tv ta ruwaito.

Adnan Oktar ya yi wa'azin ra'ayoyi masu tsauri, yayin da matan da ya kira "kittens" dinsa - wadanda da yawa daga cikinsu sun bayyana cewa an yi musu tiyatar filastic - suna rawa a kusa da shi a gidan talabijin.

An tsare shi Adnan Oktar, dan shekaru 64 a watan Yunin 2018 a matsayin wani bangare na fatattakar kungiyarsa da sashin aikata laifuka na kudi na ‘yan sandan Istanbul.

An yanke masa hukuncin daurin shekara 1,075 kan laifuka da suka hada da cin zarafin mata, lalata da kananan yara, zamba, da yunkurin leken asiri na siyasa da soja, gidan talabijin na NTV mai zaman kansa ya ruwaito.

An gurfanar da wasu mutane 236 da ake zargi a gaban shari’ar, 78 daga cikinsu suna hannun hukuma, a cewar kamfanin dillacin labarai na Anadolu.

Jawaban sun gabatar da cikakkun bayanai na karya da kuma munanan laifuka na lalata da mata.

Oktar ya fadawa alkalin da ke sauraron karar a watan Disamba cewa yana da kusan 'yan mata 1,000.

“Akwai malalar kauna a zuciyata ga mata. Kauna halin mutum ne. Kauna ce ta Musulmi,” in ji shi a wani sauraren karar a watan Oktoba.

Ya kara da cewa a wani lokaci: "Ina da karfi sosai."

Oktar ya fara zuwa bainar jama'a ne a cikin shekarun 1990 lokacin da yake shugaban wata kungiyar darika da ta afka cikin badakalar jima'i da yawa.

Tashar talabijin dinsa ta A9 da ke intanet ta fara watsa shirye-shirye a shekarar 2011, inda ta jawo masa tofin Allah tsine daga shugabannin addinan Turkiyya.

Daya daga cikin matan da ake yi wa shari’ar, wacce aka bayyana sunanta da CC, ta fada wa kotun cewa Oktar ya sha yin lalata da ita da wasu mata.

Wasu daga cikin matan da ya yi wa fyade an tilasta musu shan kwayoyin hana daukar ciki, kamar yadda CC ta shaida wa kotun.

Da aka tambaye shi game da kwayoyin hana daukar ciki 69,000 da ‘yan sanda suka gano a gidansa, Oktar ya ce an yi amfani da su ne wajen magance cututtukan fata da kuma rashin bin al’ada.

Ya kuma yi watsi da duk wata alaka da wata kungiya karkashin jagorancin mai wa’azin musulinci Fethullah Gulen da ke Amurka, wanda hukumomin Turkiyya ke zargi da kitsa yunkurin juyin mulki a shekarar 2016.

Oktar yayi imani da samuwar mahalicci wanda yayi watsi da akidar Darwin ta juyin halitta kuma ya rubuta littafi mai shafi 770 mai suna "The Atlas of Creation" karkashin sunan alkalami, Harun Yahya.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN