Alakar Gwamna da mataimakinsa ya jagule saboda neman kujerar Gwamna 2023


Alakar gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da kuma mataimakinsa, Rauf Olaniyan, ta cabe shekaru biyu bayan ‘yan siyasar sun lashe zaben 2019.

Wata majiya ta shaidawa jaridar The Nation cewa maganar takarar 2023 ce ta raba kan ‘yan siyasar.

A lokacin da Seyi Makinde yake kokarin cika alkawuran da ya dauka domin ya samu zarcewa a kan mulki, mataimakinsa ya na harin takara a 2023.

Burin Rauf Olaniyan na zama gwamna a lokacin da mai gidansa bai gama cinye wa’adinsa ba shi ne ya ke neman barka gidan gwamnatin jihar Oyo.

Bangaren mataimakin gwamna, Rauf Olaniyan, suna ikirarin cewa mai girma gwamna Makinde ba ya tafiya tare da su wajen gudanar da mulkinsa.

Majiyar ta ce gwamnan ya musanya duk wani zargi da ake yi na samun rashin jituwa, ya ce akwai ayyukan da mataimakin na sa yake jagoranta a jihar.

Shi ma mataimakin gwamnan ta bakin Omolere Omoetan, ya ce rade-radin da ake yi ba gaskiya ba ne.

A ranar Laraba, 13 ga watan Junairu, 2020, Rauf Olaniyan, ya kara tabbatar da cewa nauyin da ke kansa shi ne ya hada-kai, ya yi aiki da gwamna Makinde.

A lokacin da gwamnan ya ziyarci wani wurin killace masu cutar COVID-19, hadiman mataimakinsa sun koka cewa ba a ba Olaniyan rikon kwarya.

Akwai lokacin da mataimakin gwamnan ya shiga gidan gwamnati ya iske Makinde ba ya ofis, yayi tafiya bai sani ba, kuma bai mika masa ragamar mulki ba.

A karshen 2019 kun ji yadda wasu mutane 4000 su ka tattara su ka bar APC, su ka dawo tafiyar jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Oyo tun bayan zaben da aka yi.

‘Yan siyasar sun tasirantu ne da salon mulkin gwamna Seyi Makinde. Sababbin ‘Ya ‘yan na PDP za su yi kokari wajen kassara APC a jihar Oyo a zaben 2023.

APC ta rasa wadannan magoya baya ne a yankunan Surulere da Ogo Oluwwa a garin Ogbomoso


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN