Yadda kalaman Buhari ya fusata manyan arewa


Kungiyoyin Arewa Consultative Forum da ta Middle Belt Forum na mutanen yankin Arewa sun fusata da maganar da shugaban kasa ya yi a kan tsaro.

Mai girma shugaba Muhammadu Buhari ya fito ya na cewa an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali yanzu a yankunan Borno, Adamawa da Yobe.

Jaridar Punch ta rahoto Coalition of Northern Groups ta gammayar kungiyoyin Arewa ta na cewa babu abin da ke cikin bayanin shugaban kasar sai karya.

Shugaban Middle Belt Forum na kasa, Dr, Bitrus Porgu ya yi magana da ‘yan jarida a Jos, ya ce maganar samar da zaman lafiyan a yankunan karya ce.

Ya ce: “Boko Haram suna cigaba da kashe mutanen a wadannan yankuna, Har yau, mutanen Gwoza da Michika da su ka tsere Kamaru ba su dawo ba.”

Kungiyar ta ce an kai hare-hare a Chibok, Michika, Gwoza, Askira, Maiduguri-Damaturu da sauransu.

Sakataren yada labarai na ACF, Emmanuel Yawe, ya girgiza da kalaman shugaban kasar, ya ce babu zaman lafiyan da aka samu a wadannan yankunan.

Emmanuel Yawe ya tunawa jama’a cewa kwanan nan aka kashe manoma a Zabarmari, Borno.

Kakakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman ya ce: “Tuni mutane sun cire tsammani da sa rai daga Buhari da mukarrabansa, ko da su fito sufadi gaskiya ne.”

A yau ake samun labarin cewa wasu yan ta'addan Boko Haram sun kashe mutane shida, sannan sun kona wani coci a karamar hukumar Chibok, jihar Borno.

An yi asarar rayuka, gidaje da motoci a harin da 'yan suka kai, amma jami'an saro sun yi gum.

Suleiman da kungiyarsu ta CNG su na ganin Buhari ya zagaye kansa ne da 'yan amshin-shata da tarin mutanen da ba za su iya fitowa su fada masa gakiya.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN