Wasu cututtuka da sauro ke jawowa baya ga maleriya


Ana bayyana sauro na daga cikin ƙwari mafi hatsari a doron ƙasa.

Hakan kuwa ya faru ne saboda ganin cewa shi ne yake jawo cututtuka munana irin su zazzaɓin maleriya da ke kashe miliyoyin mutane a faɗin Afirka da sauran ƙasashe masu tasowa.

Kazalika, baya ga maleriya, akwai wasu munanan cututtukan da cizon sauro ke iya jawowa muku.

Ga wasu daga cikinsu:

Ciwon Tundurmi (Elephantiasis)

tana
Bayanan hoto,

Bincike ya gano cewa nau'o'in sauro daban-daban ke yaɗa waɗannan tsutsotsi ko tanoni

Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce kusan mutum miliyan 893 ne a kasashea faɗin Afirka wannan cutar ke yi wa barazana.

Ciwon Tundurmi na sa ƙafar mutum ta kumbura suntum, sakamakon samun wajen zama da tana ko wasu ƙanana tsutsotsi ke a ƙafar mutum

Sauro yana iya sanya wa wani cutar ta hanyar baza masa wannan tana da ya ɗauko daga jikin ami ɗauke da ita.

Bincike ya gano cewa nau'o'in sauro daban-daban ke yaɗa waɗannan tsutsotsi.

Idan wanann tana ta shiga jikin mutum, sai ta samu hanyar shigewa can cikin jikin mutum inda take hayayyafar miliyoyin ƴaƴaye da ake kira 'microfilariae' a hanyar da jini ke bi.

Wannan yanayi na ci gaba da yaɗuwa ta yadda zai haifar da tana da yawa a jikin mutum. Daga nan sai tanar ta taru ta je ta toshe babbar jijiyar jini.

Toshewar ce ke jawo kumburi a sassan jiki da abin ya shafa kamar su ƙafafu da hannaye da sauran su.

Wani bincike na Jami'ar Stanford University ya yi ya gano cewa, "ba a iya warkewa daga cutar tundrmi gaba ɗaya sai dai a yi ta magani don samun sauƙi."

Amma dai ana iya shan magunguna don rage ƙarfin ciwon da rage yawan ƙwayar cutar a cikin jini. Hakan zai hana kumburin da kuma rage barazanar yaɗa cutar ga wasu.

Cutar Shawara

A watan Nuwamban 2020 an samu ɓrkewar Cutar Shawara da ta yi sanadin mutuwar mutum 15 a wasu yankunan jihohin Delta da Enugu a kudancin Najeriya.

Sauro dangin Aedes da Haemogogus ne suke yaɗa Cutar Shawara.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Enugu Emmanuel Obi ya ce: "Irin wannan nau'in sauron sun fi cizon mutum da rana."

Ƙwararru sun ce mutum zai fara rashin lafiya bayan kwana uku zuwa shida da kamuwa da cutar, kuma idan ba a gano ta da wuri ba, mutum na iya mutuwa bayan kwana bakwai zuwa 10.

Dr Obi ya shaida wa sashen BBC Igbo cewa: Ana bai wa marar lafiyan kulawa da magani da sa ido a kansa har sai cutar ta tafi."

Babu wani taƙamaimen maganin Cutar Shawara, amma ana yin riga-kafin hana kamuwa da ita, kwana 10 bayan haihuwar mutum.

A Najeriya ma akwai dokar da aka saka cewa babu wanda zai yi tafiya zuwa wata ƙasar ba tare da shaidar cewa an yi masa riga-kafinta ba.

WHO ta ce Cutar Shawara ta zama annobar da ta shafi ƙasashen Afirka 47 da kuma wasu na yankin Amurka.

Cutar Zika

baby with zika virus
Bayanan hoto,

Cutar Zika na ta sa a haifi jariri da ɗan ƙaramin kai

An fara gano ƙwayar cutar Zika ne a jikin birrai a Uganda a shekarar 1947. Daga baya aka gano ta a jikin ɗan adam a shekarar 1952 a Uganda da Tanzaniya.

Wani sauro nau'iin Aedes ne ke yaɗa ta, amma kuma ana iya yaɗa ta ma ta hanyar jima'i, sannan uwa na iya yaɗa ta ga jaririnta.

Cutar Zika tana yin lahani ne ga kwakwalwar jariri tun yana ciki, a inda take tsumburar da ita ta kuma sa a haife shi daɗan ƙaramin kai.

A lokacin da aka samu ɓarkewar cutar a Brazil a shekarar 2016, an samu kusan mutum 200,000 da suka kamu da ita, inda aka yi ta haifar jarirai da tawaya.

Saura cututtukan da sauro ke jawowa sun haɗa da:

Zazzaɓin Dengue da zazzaɓin Chikungunya da zazzaɓin West Nile, kuma sun samo asalin sunayensu ne daga yankunan da aka fara gano su, kamar yadda Dr Sani Gwarzo wani ƙwararre a harkar lafiya ya cewa BBC.

Sannan ya ce suna da kamaceceniya ta yin zazzafan zazzaɓi da kuma zubar jini.

Yadda za ku kare kanku daga cizon sauro

Ku dinga tabbatar da tsaftace muhallinku kuma kar ku dinga barin kwata. Yawanci sauro na hayayyafa ne a cikin kwata ko ruwan da ba ya tafiya.

Ku dinga amfani da mayukan shafawa a jiki da ke kore sauro sanna ku dinga sanya tufafin da za su rufe muku jiki duka

Ku dinga amfani da maganin kashe sauro, amma ku kula kar ku yi amfani da wanda zai cutar da ku.

Ku dinga kwana a cikin gidan sauro.

Source: BBCHausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN