Shugaban Hafsun Soji, Janar Buratai ya maida raddi a kan kalaman Magauta


Shugaban sojojin kasan Najeriya, Laftana Janar Tukur Buratai, ya yi wa masu sukar manyan jami’an tsaron kasar nan raddi a kan halin rashin tsaro.

Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi magana ne bayan an huro wuta a kan cewa ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canza hafsun tsaron kasar.

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa Tukur Yusuf Buratai ya yi wannan magana ne a shafinsa na Facebook, ya na nuna cewa yanzu aka fara yaki da miyagu.

Wasu da-dama suna ganin bai dace Tukur Buratai da takwarorinsa su cigaba da zama a ofis har yanzu ba.

A shafinsa na Facebook, babban sojan ya ke cewa fadan da ake yi da ‘yan ta’adda da masu tada zaune-tsaye, zai iya kai akalla wasu shekaru 20 masu zuwa.

“Jama’a sun yi tarayya wajen rashin fahimtar abin da yakin sunkuru da ta’addanci ya kunsa. Akwai yiwuwar a kara shekaru 20 ana fama da ta’addanci.”

Buratai ya ce: “Ya danganta ne da yadda abin ya rincabe da kuma martanin da duk wasu masu ruwa da tsaki suke yi; jami'an sojoji da kuma masu farar hula.”

Hafsun sojan kasar ya ce dole mutanen gida da na kasar waje su bada gudumuwarsu a yankin.


Shugaban Hafsun Soji, Janar Buratai Hoto: www.pmnewsnigeria.com

“Akwai matukar bukata da tasirin al’umma. Dole duk su hada kai wajen shawo kan sha’anin rashin tsaron da ya ki ci, ya ki cinyewa.” Inji Janar Tukur Buratai.

Daily Nigerian ta rahoto hafsun sojin kasar ya na kira a tashi tsaye, a kawo karshen matsalar.

Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana dalilin da yasa Muhammadu Buhari ya ke ci gaba da barin shugabannin tsaro a ofis.

Garba Shehu ya ce nada shugabannin tsaro ko tsige su ikon shugaban kasa ne, kuma yana da damar ci gaba da barinsu idan har ya gamsu da kokarin da su ke yi.

Hadimin shugaban kasar ya soki kiran da wasu su ke yi na ganin an canza hafsoshin tsaron.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN