Rashin tsaro: Akasarin jihohin arewa maso yammacin Najeriya sun rufe makarantu


Kusan ana iya cewa al'ummar Najeriya sun shiga zulumi da zaman fargaba da kuma rashin tabbas tun bayan sace dalibai maza sama da 500 a makarantar sakandiren Ƙanƙara da ke jihar Katsina.

Boko Haram ta dauki alhakin yin garkuwa da daliban, ko da yake har yanzu ba a ji komai daga ɓangaren hukumomin Najeriya kan saƙon muryar da ƙungiyar masu tayar da ƙayar bayan ta fitar ba.

Wannan yanayi na matsalar tsaro ga alama ta sa wasu jihohin arewacin ƙasar ɗaukar matakin rufe makarantunsu.

Jihar Katsina ce ta fara rufe nata makarantun, sai Zamfara ta sanar da irin wannan mataki kan makarantu bakwai a yankunan da ke da iyaka da jihohin Katsina da Kaduna da kuma Sokoto.J

Jihohikamar Jigawa da Kaduna, su ma sun sanar da rufe makarantu, amma sun ce sun yi hakan ne saboda annobar korona.

Jihar Kano ta biyo baya inda a daren Talata ta sanar da rufe makarantun kwana sannan ta umarci iyaye su kwashe 'ya'yansu ba tare da bata lokaci ba. Lamarin dai ya zo ne kwana biyar, bayan sace ɗaruruwan ɗalibai a garin Ƙanƙara.

'Durkushewar yankin arewa'

A wannan shekarar ɗaruruwan mutane sun mutu a yankin arewa maso yammacin Najeriyar wanda galibin lokuta ake alaƙanta wa da ƴan bindiga ko fashi, sai dai a yanzu akwai shakku da ɗiga ayar tambaya kan ko ta'asar da ake tafkawa a wadannan yankuna na da alaƙa da Boko Haram.

Masu sharhi da masana harkokin tsaro na ci gaba da sukar shugaba Muhammadu Buhari, wanda harin baya-bayanan ya aukuwa a jihar da ya fito.

Ana gani akwai gazawa daga shugaban wajen tunkarar matsalolin tsaro da fiɗa ƴan ƙasar daga wannan hali da suka tsinci kansu.

Masana suna mai gargaɗin cewa rashin yiwa warwara tufka tun a kan lokaci na iya durkusar da yankin arewa, ganin a kulum abubuwa sake rincaɓewa suke.

Wasu na ganin shugaban babu wata damuwa tattare da shi ganin yadda ake ta yawo da hotunan bidiyo da ke nuna shi ya kai ziyara gonarsa.

"Akwai rashin nuna ƙwarewa da halin ko-in-kula, da rashin sanin mene ne shugaanci da Buhari ke nunawa," a cewar tsohuwar ministar ilimin Najeriya Oby Ezekwesili a tattaunawarta da BBC.

Tsohuwar ministar ta zargi gwamnati da nuna sake da kuma ambatar ƴan ta'adda a matsayin ƴan fashin daji. 

Wannan layi ne

Tasirin rufe makarantu

Iyayen yara da ɗaliban da dama sun bayyana takaici da wannan hali da munanan matsalar tsaro abin da ya kai ga wasu jihohi na rufe makarantu.

Ko da yake akwai jihohin da ke danganta rufe makarantu da sake dawowar annobar korona, sai dai akwai masu ganin yanayin tsaron ƙasar ne sila.

Wasu iyayye da BBC ta zanta da su da kuma ɗalibai sun nuna takaici da rokon gwamnati ta kawo karshen wannan yanayi da ake ciki ganin a baya an shafe watanni ana zaman gida saboda annoba.

Iyaye na fargabar makomar ilimi a arewa inda aka gaggara shawo kan barazanar da tsaro ke haifarwa a ƙasar.

Wannan layi ne

Shimfida

Satar mnutane domin neman kuɗin fansa abu ne da ya jima yana ciwa al'umma tuwo a ƙwarya, wannan dalili ya sanya matafiya suka rage sannan aka takaita balaguro a ƙasar.

Karuwar lamari ya sanya ana ta kokwanto da tambayar yadda masu garkuwar ke cin karensu babu babbaka, har su gaggari jami'an tsaro.

Amma satar ɗaliban ƙanƙara a yanzu ya sake baje sabon babi, inda wasu ke tambayar ko dama ƴan Boko Haram ne suka sauya salo.

Hankulan ƴan Najeriya a yanzu a tashe yake, kuma ana zama cikin yanayi na rashin tabbas la'akari da cewa a kullum labarin sauyawa yake.

A shekara ta 2009 mayakan Boko Haram suka soma kai munanan hare-hare, akasari a yankunan arewa maso gabashin Najeriya. Dubbai sun mutu, kazalika milyoyi sun rasa muhallai da tilasta musu hijira.

Iƙirarin Boko Haram na wannan lokaci kan ɗaliban ƙanƙara ya dimauta ƴan ƙasar, ganin cewa wannan ne karo na farko da aka yi garkuwa da mutane masu ɗimbin yawa a makaranta a Najeriya, bayan ɗaliban Chibok a 2014 da kuma na Dapchi a 2018.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN