Mutum 712 sun kamu da korona a ranar Kirsimeti, 4 sun mutu


Hukumar yaki da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), ta bayyana cewa an samu karin mutane 712 da suka kamu da annobar korona a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba.

Hakan na kunshe ne a cikin sabbin alkaluman da hukumar ta wallafa a shafin Twitter. Ta kuma bayyana cewa karin mutane hudu sun mutu.

Sabbin mutanen da suka kamu sun fito ne daga jihohi 20 na kasar da suka hada da:

Legas: 388

Abuja: 77

Kwara: 39

Katsina: 35

Bauchi: 33

Plateau: 22

Ogun: 18

Akwa Ibom: 16

Delta: 13

Kaduna: 12

Osun: 12

Yobe: 11

Sokoto: 10

Kebbi: 8

Enugu: 6

Edo: 5

Ondo: 3

Niger: 2

Kano: 1

Oyo: 1

Gaba daya jimlar mutane 82747 ne suka harbu da cutar a Najeriya, yayin da 1,246 suka mutu sannan a yanzu an sallami mutane 70,239 bayan sun warke.

A wani labari, an yi ma yarima mai jiran gado na kasar saudiyya, wanda shine ministan tsaron kasar, Mohammad bin Salman, allurar cutar Korona ranar Juma'a, 25 ga watan Disamba, 2020.

Bayan da Yarima ya karbi nasa, ministan al'adan kasar, Yarima Badr Farhan, ya karbi nashi rigakafin.

Ministan lafiyan kasar, Dakta Tawfiq Al-Rabiah, ya godewa yariman bisa mulkin da ya nuna wajen samarwa al'ummar kasar rigakafin.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN