Fusatattun matasa sun kashe kuma suka kone gawar wasu da ake zargin yan bindiga ne guda uku a kasuwar garin Charanci, a karamar hukumar Charanci a jihar Katsina ranar Lahadi.
Katsina Post ta labarta cewa an kama yan bindiga ne dauke da AK 47 a cikin kasuwar.
Wani ganau ya ce wani saurayi ne ya kula cewa daya daga cikin mutanen wanda suka kawo Sa domin sayarwa a kasuwar ya boye bindiga AK47 a doguwar rigar Overall coat da yake sanye da ita
Sakamakon haka jama'a suka fuskance su da tambayoyi, lamari da ya sa aka gano cewa sauran ma sun boye bindigu a cikin Overall coat da suke sanye da su.
Sakamakon haka jama'a suka far masu da duka har suka kashe su kuma suka kone gawarsu.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari