Mahara sanye da tufafin soji sun kashe mijin mataimakiyar shugaban karamar hukumar Kogi


Yan bindiga sanye da tufafin soji sun kashe Ishaku Gata mijin Mataimakiyar shugaban karamar hukumar Kogi a jihar Kogi Hon Hassana JB Ishaku.

Mutum biyar sanye da tufafin soji sun yi wa Ishaku tare da Joshua Jonah kisan gilla ta hanyar harbinsu da bindigogi yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gona a kauyen Tanahu da karfe 9:48 na safe.

David Jerry wanda dan uwan marigayi Ishaku ne, kuma yana tare da marigayi Ishaku a lokacin harin, ya ce Allah ne ya ketarar da shi wannan hari domin dai maharan sun yi masu kwanton bauna ne suka bude masu wuta ba gaira ba dalili.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN