Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Nasarawa United ta bayyana ɓacewar ɗan wasanta

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Nasarawa United ta bayyana ɓacewar ɗan wasanta


Hukumar Kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United ta sanar da cewa daya daga cikin yan wasan ta, Muhammad Hussain, ya bace, kuma ba a san inda ya ke ba.

Shugaban kungiyar Nasarawa United, Isaac Danladi ne ya bayyana haka ranar Laraba a garin Lafia, ta kafafen yada labaran kungiyar, The Punch ta ruwaito.

Danladi ya bayyana cewa dan wasan ya na da ragowar kwantaragi da kungiyar kuma ya na karbar albashin sa duk wata har kawo yanzu, kafin a neme shi a rasa.

Ya kara da cewa Hussain bai dawo kungiyar ba tun barowar su filin atisayen Flying Eagles, bayan cire su daga kofin zakarun Afirka na yan kasa da shekara 20 a kasar Benin a baya bayan nan.

Shugaban kungiyar ya gargadi duk wani mutum ko wata kungiya da ke shirin dauke dan wasan daga kungiyar da ya yi hattara, ya na mai cewa sun sanar da hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF da kuma hukumar shirya gasar firimiya halin da ake ciki.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN