Da sanyin safiyar Talata 8 ga watan Disamba, fusatattun jama'a sun kashe wasu yan fashi guda uku kuma suka banka wa gawarsu wuta a birnin Warri na jihar Delta.
Da karfe 2 na dare dubun wadannan yan fashi ta cika bayan an kama su suna aikata fashi da makami a unguwar Emeberin.
ISYAKU.COM ya samo cewa yan banga ne suka kama wadannan yan fashi, amma fusatattun matasa suka yi kukan kura suka kwace su daga hannun yan banga suka aikata masu hukuncin kato da gora ta hanyar yi masu dukan ajali kuma suka kone gawakinsu.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari