Kada ka cire takunkumin hana shigo da shinkafa, gwamnan Benue ya bukaci Buhari


Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari kada ya saurari maganan mutane na cire takunkumin hana shigo da shinkafar gwamnati daga kasashen waje.

The Punch ta ruwaito cewa gwamna Ortom ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ranar Litinin, 30 ga Nuwamba. Ya yabawa shugaba Buhari kan dokar yayinda ya ambaci muhimman riba biyu da aka ci tun lokacin da aka hana shigo da shinkafa A cewar gwamna Ortom, hana shigo da shinkafa ya harzuka manoman shinkafan gida da kuma noma gaba daya a jihar.

Ya ce wannan ne abu guda babba da gwamnatin Buhari tayi. Gwamnan ya bayyana cewa duk da cewa za'a fuskanci matsaloli da wahala na dan lokaci, manoma na samun kudi sosai yanzu fiye yadda suke samu a baya. Wani dalilin da gwamnan ya ambata shine samarwa matasa aikin yi. Ya ce matasa da dama sun koma noma kuma hakan ya taimaka. Ortom ya ce idan aka cigaba a haka, jihar Benue za ta rika samawa kasar gaba daya abinci.

A bangare guda, manoman Najeriya a ranar Laraba sun yi Alla-wadai da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na sake bude iyakokin Najeriya na kasa. Sun bayyana cewa bude iyakokin a yanzu da kayan abinci ke hauhawa abune mai hadarin gaskiya. Sun ce kasashe makwabta da suka dogara kan Najeriya wajen samun kayan abinci zasu shigo kasar kuma hakan zai sa kayan abinci ya sake hauhawa, Daily Trust ta ruwaito. R

Source: legit

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN