Jami’an Gwamnati 6 a Najeriya da a baya suka yanke jiki suka fadi a Kotu


Yadda jami’an gwamnati ke yanke jiki ko nuna halayya ta rashin lafiya a lokacin da ake bincikarsu, ba sabon abu ba ne a Najeriya.

An sha ganin ƴan siyasa ko wasu masu riƙe da muƙami na sumewa a kotu, wasu kuma na halartar kotun saman gadon asibiti ko keken guragu da nufin neman afuwa ko sassauci a shari’ar da ake masu.

Yawancinsu ana zarginsu ne da wawushe dukiyar ƙasa ko kuma almundahana.

Mun yi nazari kan jami’an gwamnati shida a Najeriya da suka yanke jiki suka faɗi a kotu ko suka halayya ta rashin lafiya.

Abdulrasheed Maina

Tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul, Abdulrasheed Maina wanda ake shari’arsa tun 2019 ya yanke jiki ya faɗi a kotun Abuja bayan sake bayyana gaban kotun a ranar Alhamis

Maina ya yanke jiki ya faɗi a kotun a yayin da ake sauraren ƙara kan tuhumarsa da ake yi kan almubazzarancin dala biliyan biyu.

Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna Maina ya yi zama irin wanda ake kira “zauna ka ci doya” yayin da ake riƙe da shi bayan ya farfaɗo.

A kwanakin baya ne dai aka kama Maina a Jamhuriyyar Nijar inda ‘yan sandan ƙasa da ƙasa suka tasa ƙeyarsa zuwa Najeriya domin ci gaba da shari’arsa bayan ya tsere daga belinsa da aka bayar a kwanakin baya.

Hukumar EFCC ce ke ƙarar Maina kan tuhume-tuhume 12, daga ciki har da mallakar manyan ƙadarori a Abuja babban birnin Najeriya.

Tsohon shugaban hukumar Neja Delta Daniel Pondei

Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) ya taɓa yanke jiki ya faɗi yayin da ake tsaka da binciken almubazzaranci da ake zargin hukumarsa da yi.

Hakan ya faru ne yayin shari’arsa a watan Julin 2020 lokacin da yake bayar da bayani ga ƴan Kwamitin Majalisar Tarayya kan Neja Delta game da yadda hukumar ta kashe biliyoyin naira.

Pondei ya kasa numfashi kuma ya ƙame a kan kujerar da yake zaune. A ƙarshe sai fitar da shugaban daga cikin ɗakin taron aka yi.

Wannan dalilin ya sa har aka jinkirta bincikensa na wani tsawon lokaci.

Haka kuma Mista Pondei ya fice daga zauren binciken ba tare da an kammala ba, sannan ya zargi shugaban kwamitin, Sanata Olubunmi Tunji-Ojo da cin hanci.

Tsohon kakakin PDP Olisa Metuh

Tsohon kakakin jam’iyyar PDP, Olisa Metuh da kotu ta yanke wa hukuncin daurin shekara bakwai ya taɓa shiga bayyana kotu saman gadon ɗaukar marar lafiya na asibiti.

An kama shi ne da laifin almundahanar kuɗi naira miliyan 400 da ake zargin ya karɓa daga tsohon ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro Kanal Sambo Dasuki zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.

Hukumar EFCC da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ce ta shigar da shi ƙara.

Sanata Dino Melaye

Sanata Dino Melaye, shi ma ya taɓa gurfana gaban wata kotun majistare a Abuja saman gadon ɗaukar marar lafiya, lokacin da yake rikici da ƴan sanda.

Ƴan sanda ne suka gabatar da shi kotu kan zargin yunƙurin kashe wani jami’insu da kuma zargin tserewa daga hannunsu a 2018.

Rikicin Dino Melaye da ƴan sanda ya ja hankalin ƴan Najeriya a lokacin.

Tsohon gwamna Ayo Fayose

Tsohon gwamnan Ekiti Ayo Fayose shi ma ya taɓa nuna yanayi na rashin lafiya a arangamarsa da jami’an tsaro.

An taɓa nuna Fayose yana kuka sharaf-sharaf yana cewa wai wani dan sanda ya yamutsa shi a lokacin tsaben gwamnan Ekiti.

Ayodele Fayose wanda ya yi gwamnan jihar Ekiti da ke kudancin Najeriya a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP, ya yi ƙaurin suna wajen yawan sukar manufofin gwamnatin Shugaba Buhari.

Tsohon gwamnan ya yi suna matuka a Najeriya saboda dambarwar da aka san shi da ita.

Tsohon ministan tsaro Bello Halliru

Tsohon shugaban Jam’iyyar PDP kuma tsohon ministan tsaro Bello Haliru Mohammed ya taɓa bayyana Babbar Kotun Tarayya a 2016 saman keken guragu lokacin da ake shari’arsa.

Hukumar EFCC ce ta zarge shi da karɓar kudi dala biliyan biyu daga ofishin tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara Sambo Dasuki, cikin kudaden da Dasukin ya shaida wa kotu cewa an ware su ne domin sayen kayan yaki.

Kuma Bello Halliru a lokacin ya isa kotun ne a kan keken guragu, a dalilin cewa ba shi da cikakkiyar lafiya.

Akwai ƴan siyasa da dama a Najeriya da ke amfani da rashin lafiya domin ƙauracewa zuwa kotu.

Wasu daga cikinsu sun haɗa da tsohon gwamnan Adamawa Bala Ngilari da tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode da tsohuwar ministar albarkatun man fetir Diezani Alison-Madueke.

BBChausa.

 


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN