Hadiza Gabon ta yi wa tsohon da ya ce yana sonta dubun arziki


Shahararriyar jarumar nan ta Kannywood, Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Gabon ta yi wa wani dattijo da ya nuna yana kaunarta sha tara ta arziki.

Jarumar ta yi wa dattijon wanda ba a bayyana sunansa ba kyautar kudi har naira dubu dari biyu.

Hakan ya faranta ran tsohon har ya bayyana cewa ya janye tare da yi mata fatan alkhari da tarin addu’o’i.

A wata wallafa da shafin Jakadiyyan_arewa_tv_ ta yi a Instagram, an jiyo dattijon na cewa:

“Alhamdulillah ma shaa Allah, Hajiya Hadiza na ga sako nagode Allah ya saka da alkhairi, ubangii Allah ya bar zumunci kuma kamar yadda kika mun Allah ya miki da alkhairi.

“Kuma kamar yadda kika fada idan biki ya zo za a sanar dani, hakika na yarda na zama uba nagari, albarkar annabi ina daya daga cikin uba iin shaa Allah ranar biki, Allah ya nuna mana lokaci.

“Na karbi kudi naira dubu gari biyu Allah ya saka da alkhairi, Allah ya ji kan mahaifa, nagode, Allah ya kara kusanci da hazaka.

“Da farko dai dattijon ya nuna ra’ayinsa na son jarumar, inda ya roki Allah ya mallaka masa ita a matsayin matarsa ta sunnah.”


A wani labari, Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Maryam Booth, ta tabbata a gwarzuwar jarumar Africa Movie Academy Awards, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Maryan Booth ta samu nasarar ne sakamakon rawan da ta taka a wani fim mai suna The Milkmaid, inda ta bige Chairmaine Mujeri (Mirage), Linda Ejiofor (4th Republic) da wasu mutane hudu.

A cike da murnar wannan nasarar, jarumar ta wallafa rubutu a shafinta na Instagram kamar haka: "Ina taya kaina da iyalan fim din milkmaid murna. Muna fatan karin nasarori, sai mun hadu nan gaba a Oscar."

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN