Gwamnan jihar Borno Zulum ya bankado ma'aikatan bogi fiye da 20,000


Gwamnatin jihar Borno ta bankaɗo malaman bogi da ma'aikatan ƙananun hukumar dake jihar kimanin 22,556 a wani yunkurin tantance ma'aikata da malamai da gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum, ya bayar da umarnin aiwatarwa.

Alƙaluman sun nuna kimanin ma'aikatan bogi 14,662 aka gano a ƙananun hukumomin jihar yayin da aka gano wasu malaman karya har 7,794 a ɓangaren ilimi.

Da ya ke gabatar da rahoton, shugaban kwamitin tantance malaman firamare, Dr. Shettima Kullima, ya ce, tantancewar ta samarwa jihar rarar kuɗi sama da miliyan 183 da suke zurarewa a iya ɓangaren malaman firamare kaɗai dake ƙananun hukumar 27 dake faɗin jiha.

Bayan karɓar rahoton ne kuma gwamna Zulum, ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne don inganta harkar ilimi a jihar Borno, kasancewar gwamnatinsa ta baiwa harkar ilimin firamare fifiko.

An fara tantance ma'aikata a jihar ta Borno tun a shekarar 2013 inda aka samo dubbanin ma'aikatan bogi.

Gwamna Zulum ne ya yanke shawarar faɗaɗa tantancewar har zuwa ma'aikatan ƙananun hukumomin jihar Borno guda ashirin da bakwai.

A ranar Laraba ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamna Zulum ya ratsar da sabbin zababbun shugabanninn kananan hukumomin jihar Borno 27.

Daga cikin sabbin shugabannin kanananan hukumomin da aka rantsar akwai Farfesoshi biyu da wani mai digiri da digirgir (PhD).

Kazalika, Farfesa Zulum ya bayar da umarnin sakarwa kananan hukumomin jihar Borno dukkan kudadensu kamar yadda dokar kasa ta bukata.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN