Farashin kwanon shikanfa da ake nomawa a gida da ake kira Ba Ingila ya sauko zuwa Naira dari hudu da talatin sabanin makonnin baya da farshinsa ya kai har Naira dari hudu da tamanin.
Kazalika shinkafa da ake nomawa a gida da ake kira Bahausa, ana sayarwa Naira dari hudu da tamanin a kasuwar wucin gadi na yan shinkafa wanda mafi yawansu yara ne da ke shigowa garin Birnin kebbi da shinkafa daga kauyen Kola kuma suke baje shinkafarsu a unguwar Rafin Atiku.
Wakilin mu ya kula cewa yan sana'ar shinkafa daga babban kasuwar Birnin kebbi suna zuwa wannan kasuwan yan shinkafa a Rafin Atiku domin sayen shinkafa da yawa da sanyin safiya. Bayanai sun nuna cewa sukan sayar da shinkafar a Naira dari hudu da hamsin a babban Kasuwa.
Kazalika wakilin mu ya kula cewa akasarin shinkafar tana da kyau, sai dai mafi yawa shinkafa da ake sayerwa bai bushe kau ba, saboda bayanai sun nuna cewa kai tsaye ake kawo shinkafar daga Masussuka.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari