A cigaba da yekuwar samarda tsabtatatcen abinci daga masu sayarwa zuwa ga masu saya da kungiyar Bright Girls ke yi a kananan hukumomi 21, yau 9 ga watan Disamba, 2020. Hon. Yahaya Bello ya karbi bakuncin Kungiyar ya kuma jinjina mata na yin wannan yekuwar tare da bayar da horo da shawarwari da kungiyar ke yi ga masu sana'oin jimaka, kamarsu Nama, zogale, Kifi, kosai, shanya shinkafa a titi ba tsabta da sauransu.
Shugaban karamar hukumar ya zagaya da kungiyar cikin kasuwa, tare da wakilin Mai girma sarkin Koko, Sarkin kudu Alh. Ibrahim, da kuma Daraktan Lafiya Alh Sala Koko, hadi da tawagar kansiloli na karamar hukumar koko Besse.
Bayan Kungiyar ta bayar da horo da shawarwari a kan yanda za'a yi ma'amala da kudi da abinci da kuma hannayen sana'a, ta raba bokitai ga masu sana'ar hakin gwabe.
Kungiyar tare da tawagar Shugaban karamar hukumar, sun kai ziyara ga mata masu sana'ar Gumi. A nata jawabi, Hajiya Luba Sulaiman, shugaban Kungiyar ta jihar Kebbi, bayarda horo akan yadda za'a sarrafa Gumi ba tare da duwatsu, kasa ko kuma wata kazanta ta shiga ba. Ta rabawa yan sana'ar Gumi manyan ledodi da za su yi anfani da shi mai makon shanyata a titi dabbobi na hawa, da motoci da mutane, wanda hakan na iya janyo nan take mai saye bayan ya dafa ya kamu da cutar Appendix.
Shugaban karamar hukumar Koko-Besse Hon Yahaya Bello, ya Umurci masu sana'ar Gumi da sauran Kayan cimaka, da su yi anfani da wannan horo da kungiyar bright Girls ta bayar. Ya kuma bayar da nashi tallafi ga kungiyar. Ya yaba mata akan wannan yekuwar da ta ke yi.
Shima Daraktan Lafiya, Alh Sala Koko, ya yi muhimman bayanai da kuma bada misallai na cutututtuka da hatsari ga rashin tsabta ga abubuwan da mu ke ci.
Daga Karshe, Sakataren Kungiyar Abubakar Abk, ya yi kira ga Shugaban karamar hukuma da ya bayar da muhimmanci ga wannan horarsuwa domin a ci gaba da hakan a kuma sanya kulawa wurin ganin masu sana'oin cimaka sun mai da hankali da tsabtar sana'arsu , jikinsu da kuma wurin sana'ar su.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari