Dakarun sojin Najeriya za su sauya salon yaki da Boko Haram da 'yan bindiga


Dakarun sojin Najeriya za su sauya salon yaki da Boko Haram da 'yan bindiga

A ranar Alhamis, hedkwatar tsaro ta ja kunnen 'yan ta'adda, 'yan bindiga , masu garkuwa da mutane da duk wasu masu aikata laifi da ke sassan kasar nan da su tuba tare da gujewa aikata laifukan kafin dakarun sojin su far musu a 2021.

Shugaban fannin yada labarai na dakarun sojin, Manjo Janar John Enenche, a wani taron manema labarai a Abuja, ya ce a tudu, iska da ruwa duk sun fara sauya salon yakar 'yan ta'adda da masu kai musu bayanai, The Nation ta ruwaito.

Ya ce, "Mayakan ta'addancin Boko Haram, 'yan bindiga da dukkan sauran masu laifuka gara su tuba a yayin da za mu shiga 2021. Babu shakka sakon da muke da shi ga 'yan ta'adda shine, kai tsaye kun saka hannu a tikitin mutuwarku saboda aiki ne da dole mu aiwatar.

"Kamar yadda aka karfafa mu, mun saka hannu a kan aikin kare kasarmu da 'yan kasan baki daya. Rayuwa za ta koma daidai ta yadda tattalin arziki da sauran rayuwa za ta dawo.

"Ga wadanda za su sauya hali kafin sabuwar shekara, muna basu damar yin hakan. Har yanzu kofofi a bude suka garesu don su tuba. Su miko kansu ga jami'an tsaron da ya dace."

A wani labari na daban, Jigon jam'iyyar APC, Sanata Abba Ali, ya yi martani a kan kara lalacewar tsaron kasar nan. Ya ce shugaan kasa Muhammadu Buhari ya gaji wadannan matsalolin ne daga jam'iyyar PDP.

Ali, wanda ya yi magana daga Katsina, ya bayyana hakan a ranar Laraba ta wata hirar wayar tafi da gidanka da yayi da gidan talabijin na Chhannels TV a shirin siyasarmu a yau.

"Rashin tsaron da ke addabar kasar nan ba tun yanzu yake ba. An gaje shi ne daga jam'iyyar PDP tun lokacin da suke mulki," mamba a kwamitin rikon kwarya na APC yace."

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN