Da dumi dumi: Mayakan Boko Haram sun dauki alhakin harin Zabarmari


Kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta dauki alhakin harin da aka kai garin Zabarmari na jihar Borno. A wani bidiyo da ta saki a ranar Talata, kwamandan kungiyar ya yi jawabi a faifan inda ya bayyana cewa sun aiwatar da kisan kiyashin ne domin rama kisan mambobinsu da sojojin Najeriya suka yi. Kungiyar ta gargadi yan farar hula da su guji yin liken asiri a kansu, shafin HumAngle ta wallafa a Twitter.

A halin yanzu, biyo bayan kisan manoma 43 a jihar Borno wanda yan Boko Haram suka yi, an bukaci gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar sauya tsarin tsaro a Najeriya. Dr. Ahmad Lawan ya yi kiran ne a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba, lokacin da ya jagoranci tawagar Shugaban kasa domin yi wa gwamnati da mutanen Borno jaje kan mummunan lamarin, jaridar The Sun ta ruwaito.

A cewar Lawan, tsarin da ake dashi a kasa baya aiki, inda ya kara da cewa gwamnati na bukatar samun sabbin manufofi da kuma ganin yadda tsarin tsaron zai inganta. A gefe daya kuma, Garba Shehu, babban mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kafofin watsa labarai, ya ce kiraye-kiraye da ake yi na a sallami shugabannin tsaro baya kan layi.

Source: Legit



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN