Batanci ga Annabi: Kotu ta umurci a sakin Mubarak Bala, ta ce a biya shi diyya


Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bada umurnin sakin Mubarak Bala, wanda ya yi amfanin da shafinsa na Facebook ya wallafa wasu rubutu da ake ganin batanci na ga Annabi Muhammad (SAW), Daily Trust ta ruwaito.

An kama, Bala, shugaban Humanist Association of Nigeria, a watan Fabrairu a gidansa da ke Kaduna bayan wasu lauyoyi sun shigar da kara a kansa inda suke zargin ya yi wa Annabi Muhammad batanci a shafinsa na Facebook.

Yan sandan jihar Kaduna suka kama shi sannan daga bisani aka mayar da shi hannun yan sandan jihar Kano a ranar 2 ga watan Mayun 2020.

Da ya ke yanke hukunci kan korar da lauyoyin Bala suka shigar na zargin keta hakkinsa na bil adama, Mai shari'a Inyang Ekwo ya ce tsare Bala da 'yan sanda suka yi na tsawon watanni ya keta hakkinsa na 'yanci, adalci, zirga-zirga da 'yancin tofa albarkacin bakinsa.

"Rashin barin wanda ake zargi ya gana da lauyoyinsa keta hakkinsa na adalcin shari'a be da samun lauya kamar yadda ya ke a karkashin sashi na 34 da 35(2) a karkashin kudin tsarin kasa ta 1999."

Alkalin ya kuma umurci rundunar 'yan sanda su biya naira 250,000 ga wanda ake yi karar.

Mubarak Bala ya dade yana sukar addini tun bayan ridda daga addinin musulunci a shekarar 2014.

An kuma gano cewar an iyayensa sun taba kai shi zuwa asibitin kwakwalwa a kan tilas a Kano amma daga bisani aka sako shi kuma tun lokacin ya cigaba da samun barazanar kisa.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN