Babban magana: Rarara ya shiga matsala kan sanya matar aure a bidiyon wakarsa


A kwanan ne wata kotu ta bukaci a binciki shahararren mawakin siyasan nan mazaunin Kano, Dauda Kahutu Rarara, bayan ikirarin cewa ya yi amfani da matar aure a daya daga cikin bidiyon da ya saki a kwanan nan.

A cewar rahotanni daga jaridar The Guardian, an yi zargin cewa Rarara ya yi amfani da matar aure mai shekaru 20, Maryam Muhammad, a bidiyon wakarsa mai suna JAHATA JAHATA TACE.

Ta kuma bayyana cewa wata kotun shari’a ta bukaci ayi binciki mawakan a kan haka.

An tattaro cewa mijin Maryam, Abdulkadir Inuwa, ya shigar da kara da kuma ikirarin cewa mawakin ya hade da matarsa a sirri.

Rahoton ya kuma yi ikirarin cewa Maryam ta watsar da mijinta a gidansa jim kadan bayan aurensu kawai sai ya gano ta a bidiyon wakar mawakin.

Alkalin, Sarki Yola, ya kuma bayyana cewa ikirarin mawakin na cewa bai san Maryam matar aure bace bao isa a yi watsi da karar wanda Inuwa ya shigar ba. Sai dai ya umurci yan sandan da ya bincike lamarin sannan su gabatarwa da kotu sakamakon bincikensu.

Alkalin ya kuma bukaci yan sanda akan su aika sammaci ga mawakin da furodusansa don binciken lamarin.

A wani labari na daban, Allah ya yiwa shahararren malamin nan na addinin Musulunci da ke Najeriya, Sheikh Ahmed Lemu rasuwa.

Shehin malamin ya rasu ne a safiyar yau Alhamis, 24 ga watan Disamba a garin Minna, babbar birnin jihar Niger.

Ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN