Atiku ya fadi abin da PDP za ta yi don kwashe kafafun APC a 2023


Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayar da bayani kan yadda jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za ta iya yin nasara a zaben 2023.

Dan siyasan wanda yayi takarar kujerar Shugaban kasa karkashin jam’iyyar ya ce doe PDP ta hade domin samun nasara a zaben 2023, Vanguard ta ruwaito.

Ya bayar da shawarar a ranar Talata, 29 ga watan Disamba, a wani taron siyasa a karamar hukumar Afikpo ta kudu da ke yankin Ebonyi ta kudu.

Tsohon mataimakin Shugaban kasar ya ce:

“A matsayinmu na jam’iyya domin ci gaba da samun nasara a zabukanmu na gaba ya zama dole PDP ta ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da hadin kai a dukkan mataki, domin hadin kai shine mabudin nasara a zabenmu, muna da yawan da ake bukata, mutane, karfi, dabaru da shugabanni a jihar Ebonyi.”

A cewar jaridar Leadership, Atiku ya ce PDP na kara karfi a jihat Ebonyi. Ya bukaci mambobin jam’iyyar a jihar da su ci gaba da jajircewa ta fuskacin matsaloli.

A wani labari, babbar kungiyar zamantakewa da siyasa, kungiyar tuntuba ta arewa (ACF), ta kwarmata cewa yanzu da rakuma ake amfani wajen shigo da makamai yankin arewa.

ACF ta bayyana cewa ana amfani da Rakuma wajen safarar manyan bindigu na RPG da bindigun harbo jirgin sama zuwa Nigeria ta kan iyakokin da ke arewa.

Cif Audu Ogbeh, shugaban ACF, shine ya bayyana hakan a cikin wani jawabi mai dauke da sa hannunsa wanda ya fitar ranar Alhamis.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN