An tube shugaban karamar hukuma sai gajeren wando, Kotu ta tura shi Kurkuku, duba dalili


Wata Kotun Majistare a birnin Asaba na jihar Delta, ta tasa keyar shugaban karamar  hukumar Panti mai suna Perez Omoun zuwa Kurkuku bisa tuhumar shi da keta haddi tare da cin zarafi ta hanyar shiga gidan Kwamishinan albarkatun lantarki na jihar Basil Ganagana.

An yi zargin cewa Omoun ya shiga gidan Kwamishinan ranar Lahadi 13 ga watan Disamba, ya tayar da hankalin jama'ar gidan da makwabta ta hanyar barnata dukiya da motoci a gidan. Kazalika an yi zargin cewa ya farmaki direban Kwamishinan.

An gurfanar da Omoun a gaban Kotun Majistare a garin Asaba ranar 16 ga watan Disamba. Daga bisani Kotu ta tura shi zuwa Kurkuku kafin ranar zaman Kotun na gaba.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN