Abubuwan da suka yi tashe a shekarar 2020 a Tuwita a Najeriya

Abubuwan da suka yi tashe a shekarar 2020 a Tuwita a Najeriya


A duniya baki daya, shafukan sada zumunta sun zamo wata muhimmiyar kafa da masu amfani da su ke bayyana ra'ayoyinsu da isar da sakonni. Kusan a iya cewa ma, shafukan su ne hanyoyin da aka fi saurin samun bayanai a fadin duniya a yanzu.

Amfani da hashtag # na taimakawa sosai wajen ganin sakon mai amfani da shafin ya yi saurin bayyana a jerin sakonnin da ake wallafawa musamman a shafukan Twitter da Instagram inda nan ne amfani da # ke da muhimmanci.

Haka kuma, kirkirar maudu'I na kara yayata jigo ko wani abu da ke faruwa, ya sa nan da nan ya yadu a shafin har a san da shi.

A wannan shekarar ta 2020, an yi amfani da # da dama a shafin Twitter don isar da sakonni kan abubuwa da dama da suka faru a Najeriya, kuma wannan makalar za ta duba wasu daga cikin manyan maudu'an da suka yi fice sosai a shafin na Twitter.

#Covid19

An gano mutum na farko mai dauke da cutar Korona a Najeriya ne a watan Fabrairun 2020 kuma jim kadan bayan sanar da hakan ne aka fara yayata maudu'in #Covid19Nigeria.

An rika amfani da #Covid19 da #Covid19Pandemic da #Coronavirus wajen aika sakonni dangane da annobar.

Kamfanin Twitter ya ce an yayata maudu'in #Covid19 da makamantansa fiye da sau miliyan 400 tun daga farkon billar cutar ya zuwa yanzu.

Haka kuma, har yanzu Hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka a Najeriya na amfani da #Covid9 wajen aika sakonninta da suka danganci cutar.

#EndSars

End Sars

A watan Oktoba ne aka fara zanga-zangar adawa da cin zarafin da aka ce 'yan sandan Najeriya na yi wa matasa a kasar.

Fara zanga-zangar a tituna ke da wuya shafukan sada zumunta ma suka dauka da batun na #Endsars kuma an shafe sama da mako biyu ana yayata wannan maudu'i.

A wani lokaci ma, sai da ya zama maudu'i mafi shahara a duniya inda har shugaban kamfanin Twitter Jack Dorsey ya yi amfani da maudu'in kuma ya sa aka kirkiro wani hoton hannu a dunkule mai launin tutar Najeriya da ke bayyana tare da maudu'in idan aka yi amfani da shi a Twitter.

Wannan mataki ya faranta ran 'yan Najeriya masu yaki da rundunar SARS kuma nan da nan wasu fitattun mutane kamar mawaka da 'yan fim na Amurka kamar su Rihanna da Trey Songs su ma suka wallafa sakonni tare da amfani da maudu'in.

Maudu'in #Endsars ya sa hankalin kasashen duniya da dama ya karkata kan Najeriya duba da irin koke koken da matasan kasar suka rika yi ta hanyar amfani da maudu'in.

#LekkiMassacre

A yammacin ranar 20 ga watan Oktoba ne zanga-zangar #Endsars ta kai kololuwa a lokacin da wasu da ake zargin jami'an tsaron Najeriya ne suka bude wa daruruwan masu zanga zangar wuta a unguwar Lekki da ke jihar Legas.

Hotunan bidiyon da wasu masu zanga-zangar suka dauka a lokacin an jiyo karar wani abu mai kama da bindiga sau da yawa, sannan an ga mutane da raunuka a jikinsu.

Amma rundunar sojin Najeriya ta musanta wannan zargin inda ta ce jami'anta ba su yi harbi a unguwar Lekki ba.

Nan da nan masu amfani da shafin Twitter suka fara amfani da wannan maudu'in na #LekkiMassacre wanda ke nufin harbe harben Lekki.

An ta yada hotuna da bidiyo da dama tare da wannan maudu'in, sannan an yi ta kira ga gwamnatin Najeriya da jami'an tsaronta bisa abin da wasu suka ce 'laifukan tauye hakkin bil'adama'.

#LekkiMassacre ya mamaye shafukan Twitter da Instagram a dan kankanin lokaci kuma manyan kafofin yada labarai na duniya sun yi amfani da shi.

#SecureNorth #EndNorthBanditry

A daidai lokacin da ake batun #Endsars a Najeriya, wasu 'yan Arewacin kasar sun yi amfani da tagomashin da masu kira da a kawo karshen rundunar SARS suka samu a fadin duniya, suka kirkiri maudu'in #SecureNorth wato A Tsare Arewa da #EndNorthBanditry wanda ke nufin A Kawo Karshen 'Yan Bindiga a Arewa .

Yankin arewacin Najeriya ya dade yana fuskantar rashin tsaro musamman ta bangaren satar mutane don kudin fansa da barayin daji da kashe kashen 'yan bindiga da dai sauransu.

'Yan arewacin kasar da dama sun yi wa zanga zangar #EndSars kallon wani abu da ya fi shafar kudancin kasar kuma a zahiri a yankin ne zanga zangar ta fi karbuwa.

Asali ma, an samu 'yan yankin arewa da dama da suka shirya tasu zanga zangar ta musamman da ke fatali da bukatun masu zanga zangar #EndSars, inda suka ce su ba su ga laifin rundunar SARS ba.

Don haka sai wasu matasan Arewa suka yayata maudu'in #SecureNorth da #EndNorthBanditry a shafukan Twitter da Instagram sannan suka yi tattaki a titunan wasu jihohin kasar don jawo hankalin gwamnati da jami'an tsaro kan lamarin da suka ce yana nema ya durkusar da yankin arewa.

An yi amfani da maudu'an biyu sosai, sai dai a iya cewa bai samu karbuwar da #Endsars ya samu ba.

#EndASUUStrikeNow

Tun a watan Maris din wannan shekarar ne Kungiyar Malaman Jami'o'I ta Najeriya wato ASUU ta shiga yajin aiki, bisa abin da kungiyar ta ce rashin mayar da hankalin gwamnati kan jami'o'in kasar.

Sannan kungiyar ta bukaci gwamnati ta biya malaman jami'a sauran alawus alawus dinsu da ba ta biya ba yayin da ita kuma gwamnatin ta ki biya wa kungiyar bukatunta.

Rashin janye yajin aikin da wuri ya sa dalibai suka fara yayata maudu'in #EndASUUStrikeNow wato A Kawo Karshen Yajin Aikin Kungiyar ASUU yanzu yanzu.

Daliban sun ta aika sakonni suna kira ga gwamnati da ASUU su daidaita saboda sun gaji da zaman gida.

#BringBackOurBoys #KankaraBoys #KankaraAbduction

Kankara

A daren Juma'a 11 ga watan Disambar 2020 ne 'yan bindiga suka afka wa makarantar sakandire ta kwana da ke garin kankara a jihar Katsina kuma suka yi awon gaba da samari sama da dari uku.

Wannan lamari ya jefa Najeriya cikin rudani kuma ya sa an tuna da sace 'yan matan makarantar Chibok 276 da kungiyar Boko Haram ta yi a shekarar 2014.

Nan da nan shafukan sada zumunta suka dauka dumi da batun sacen daliban na kankara kuma aka fara amfani da #BringBackOurBoys wato A Dawo mana da Samarinmu don isar da sakonni kan lamarin.

Bayan sace 'yan matan Chibok, maudu'in #BringBackOurGirls (A Dawo mana da 'Yan matanmu) ya yi tashe a duniya baki daya inda fitattun mutane kama daga shugabnnin kasashe zuwa attajirai da mawaka da 'yan fim na kasashen waje sun yi amfani da maudu'in.

Source: BBCHausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN