A villa ake iskanci na gaske: Aisha ta mayar da martani a kan gargadin shugaba Buhari


Fitacciyar 'yar gwagwarmaya kuma daya daga cikin jagororin zanga-zangar EndSARS, Aisha Yesufu, ta mayar da mayar da martani a kan gargadin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi wa ma su zanga-zanagar EndSARS a ranar Litinin.

Shugaba Buhari ya yi gargadin ne a yayin da wasu matasa su ka kara fitowa domin sake farfado da zanga-zangar EndSARS a karo na biyu a Lagos da Osun. Buhari ya ci al washin yin maganin duk wani salon iskanci.

A cikin wani martani da ta fitar jim kadan bayan gargadin da shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na tuwita, Aisha ta bayyana shugaba Buhari a matsayin matsoraci tare da bayyana cewa a fadar shugaban kasa (Aso-Villa) ake aikata babban iskanci.

"An nemi matsoracin an rasa a lokacin da mayakan kungiyar Boko Haram su ka kashe manoma 78 saboda kawai an kama daya daga cikinsu.

"A Aso Villa ake iskanci na gaske kuma shugaba Buhari ke jagorantarsa! kamar yadda Aisha ta wallafa a martanin da ta wallafa a kan sakon da Buhari ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Legit.ng Hausa, a kwanakin baya, ta rawaito cewa Dr.Chinonso Egemba wanda aka fi sani da Aproko Doctor da ƴar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, sun maida martani kan ƙarar da Kenechukwu Okeke, ya shigar dasu akan marawa masu zanga-zangar EndSARS baya.

Rahotanni sun bayyana cewa Okeke ya shigar da ƙarar masu goyawa zanga-zangar EndSARS baya a babbar kotun tarayya dake Abuja.

Okeke lokacin da yake bayyana dalilin shigar da ƙarar yace yayi haka ne don wanzuwar tsaro,kare al'umma da kuma dawo da lumana a cikin al-umma.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN