2023: Primate Ayodele ya ce Allah bai aiko Tinubu don ya shugabanci Najeriya ba


Zamowar Bola Tinubu, babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), na zama Shugaban kasar Najeriya na gaba ba mai yiwuwa bane kamar yadda Primate Babatunde Elijah Ayodele ya kaddamar a wahayinsa.

Primate Ayodele, Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church da ke Lagas ya fada ma Legit TV a wata hira cewa Allah baya goyon bayan shugabancin Tinubu.

A cewar faston, duk wani yunkuri da jigon na APC zai yi don takarar Shugaban kasa ba zai cimma nasara ba.

Ya ce:

“Shugabancin Tinubu zai sha kunya... saboda Allah bai aiko Tinubu don ya shugabanci Najeriya ba.”

https://www.youtube.com/watch?v=EZ8qCP-pG3U

A wani labarin, mun ji cewa kungiyar CAN ta Kiristocin Najeriya ta fito ta kare babban limaminta a Sokoto, Bishof Mathew Hassan Kukah.

Kungiyar ta CAN ta ce a jawabin da Mathew Hassan Kukah ya yi na bikin Kirismeti, babu inda ya soki Musulunci ko kuma ya yi kiran ayi juyin-mulki.

CAN ta zargi gwamnatin tarayya, shugaban kasa da kuma shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola da neman juya maganar da Faston ya yi.

A gefe guda, Dino Melaye, tsohon sanata, ya gargadi Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yunkurin kama limamin Katolika na Sokoto, Mathew Kukah, kan sukar gwamnati mai ci.

Wasu kungiyoyi a kasar sun caccaki limamin kan zargin Shugaba Buhari da son kai.

Kungiyar matasan Tiv sun zargi limamin da kira ga tunkudar da shugaban kasar sannan suka bukaci hukumomin tsaro su binciki malamin.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN