Zaben Amurka: Joe Biden na shirin nada jami'an gwamnatinsa, Trump ya ce kar ya kuskura


Yayin da har yanzu ake ci gaba da kirga kuri'un da aka kada a zaben Amurka da aka gudanar a ranar Talata 3 ga watan Nuwamba, 2020, shugaba Trump ya gargadi abokin takararsa Joe Biden a kan kada ya soma ayyana kansa a matsayin wanda ya samu nasara.

BBC ta ruwaito cewa Joe Biden na shirin nada jami'an gwamnatinsa a rahotunta na safiyar Asabar 7 ga watan Nowamba.

Wannan kuwa na zuwa ne a yayin da sakamako kuri'un da ake kirga wa ke nuna cewa Joe Biden din ke kan a gaba a mafi yawancin jihohin da suka rage a kammala kidaya kuri'unsu.

Shugaba Trump din ya wallafa a shafinsa na tuwita cewa, kararrakin da ya shigar a kan kuri'un da aka kirga yanzu za su fara aiki.

Mr Trump din dai ya yi gargadi bayan da tun a baya ya ayyana kansa a matsayin wanda zai samu nasara a zaben.

Tana kasa tana dabo a game da nasarar shugaba Trump din, kasancewar jihohin da suka rage ba a kammala kidaya kuri'unsu ba kamar Pennsylvania da Geogia da Nevada da kuma Arizona, Biden din ke kan gaba a yawancinsu kodayake komai zai iya canjawa saboda rashin tabbas a kuri'un da suka rage ba a kirga ba.

Yawancin kuri'un da aka kada ta akwatin gidan waya da ake kirgawa tun daga ranar da aka yi zaben kasar, Biden ne ke samun nasara a kansu.

Tuni dai ofishin kampen din Trump din ya shigar da kara inda yake kalubalantar sakamakon kuri'un da ake kirgawa a jihohi hudu da idanun duniya ke kansu.

Ofishin kampen din dai na zargin cewa an yiwa Trump din magudi, amma kuma duk da hakan ba a fasa ci gaba da kidaya kuri'un ba.

Masu sharhi dai na cewa sakamakon zaben Amurka ga dukkan alamu zai iya daukar wani lokaci kafin a sanar da wanda ya samu nasara akasin zabukan baya da ba a daukar wani lokaci ake sanar da wanda ya samu nasara a zaben.

Tuni dai Ƙwamitin yaƙin neman zaɓen Mista Trump ya buƙaci a sake ƙirga ƙuri'un da aka jefa a jihar Wisconsin sakamakon "wasu abubuwa da ba daidai ba da aka gani" a ranar Laraba.

Babu wani tabbaci ko yaushe za a sake ƙirga waɗannan ƙuri'u, sai dai, hakan ba zai faru ba sai jami'an jihohin sun kammala tantance waɗannan ƙuri'un. Wa'adin da aka bai wa jihohi kan wannan lamarin shi ne 17 ga watan Nuwamba.

Source: BBC


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN