Yadda Naira 100 Ta Jawo Fadan Kabilanci A Garin Nsukka

Fadan kabilanci da addini da ya faru a ranar Juma’a 31 ga Oktoban da ya gabata inda wadansu matasa da ake zargin zauna gari banza ne suka far wa al’ummar Arewa mazauna garin Nsukka da ke Jihar Enugu, ya faru ne a kan Naira 100 kacal.

Sarkin Hausawan Nsukka, Alhaji Muhammadu Azaga ya shaida wa wakilinmu cewa Naira dari ce ta jawo rikicin bayan wata yarinya mai suna A’isha ta sayi tumatiri ta dauko dan Keke NAPEP ya kai mata shagonsu.

Ya ce bayan ya kai mata an sauke kayan maimakon ta biya kudin dakon Naira 100 kamar yadda suka yi jinga sai ta ki biya, lamarin da ya haifar da tankiya a tsakaninsu.

A cewar Sarkin an ce da mai Keke NAPEP din ya tsaya a biya shi kudin, amma ya ki karba daga nan ne rikicin ya fara har ya buwaya ya kai wadansu matasa suka yi amfani da wannan dama suka far wa ’yan Arewa suka farfasa shagunansu tare da kwashe musu kadarori.

Alhaji Muhammadu Azaga ya ce “Magana dai magana ce ta wata yarinya mai suna A’isha da dan Keke NAPEP; maganar kudi ce tsakaninsu da mai babur din da ya kawo ta a kan Naira 100. An ce ma za a biya kudin yarinyar ta ki yarda, gaskiya haka ne sanadi”.

Alhaji Muhammadu Azaga ya ce bayan ya dawo daga Obolo (Obolafor) ne ya samu labarin faruwar haka.

Ya ce komai ya wuce ana zaune lafiya wadanda aka lalata musu tebura an tayar da su ana gyarawa, wadansu kuma sun tafi gida, amma na ce su dawo na bude kayana ma yau (Laraba).

Shugabanni sun yayyafa wa rikicin ruwa

Ya ce Shugaban Karamar Hukumar Nsukka, Mista Cosmos Ugwu ya kai musu tallafin shinkafa, sukari da taliyar Indomie.

Ya bayyana cewa rumfunar ’yan Arewa da aka lalata za su kai 100, amma ba zai iya kididdige asarar da aka yi ba saboda wasu shagunan an kwashe kayan ciki an tafi da su.

Sarkin Hauswan ya ce gwamnati ta dauki matakin ba su kariya domin Kwamandan ’Yan Sanda na yankin da shugaban karamar hukumar sun yi kokari “Muna zaune da su kwana ma muke yi da su”, inji shi.

Ya ce shugaban ’yan sanda ya zo daga Enugu, sojoji ma sun yi kokari tare suke kwana da su.

Alhaji Muhammadu Azaga, ya ce babu asarar rai a rikicin sai dai wadanda suka samu raunuka an kai su asibiti wadansu an sallame su wadansu na can, kuma Bishop-Bisho ne suka biya kudin yarinyar gaba daya.

Gwamnati za ta gina masallatan da aka lalata

Sannan ya yi kiran a zauna lafiya da cewa, “Wadanda suke Kudu mazauna Arewa su sani idan wata matsala ta taso muna nan Kudu tana shafar mu, idan kuma daga nan Kudu ta tashi tana shafar mu don haka a zauna lafiya a ci gaba da yin addu’ar Allah ya zaunar da mu da kasarmu lafiya,” inji shi.

Source: Jaridar Aminiya

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN