Shugabannin Amurka 10 kacal suka fadi a zaben tazarce a tarihi, da alamun Trump zai zama na 11 (Ga jerinsu)


A tarihin Amurka, shugabannin kasa suna samun nasarar tazarce bayan karewar wa'adinsu na farko saboda irin ayyukan da suka yi.

Amma ba haka ake gani tattare da Donald Trump ba saboda lokacin da ya kaddamar yakin neman zabensa a 2019, maki 43% kadai ya samu, cewar Gallup.

Business Insider ya bayyana cewa tun daga lokacin makin ke cigaba da sauka.

Binciken Gallup a watan Satumba da Oktoba ya nuna cewa makin da Trump ya samu bai wuce 42% zuwa 44%

Watanni baya, bincike ya nuna cewa da wuya Trump ya zarce saboda matsin tattalin arzikin da kasar ta shiga da kuma yadda Trump ya gudanar da yaki da cutar COVID-19.

Trump na bayan Biden a manyan jihohi irinsu Michigan, Wisconsin, Pennsylvania da Florida, duk da cewa ya lashe wadannan jihohi a zaben 2016.

A karshe, Trump na iya shiga jerin shugabannin Amurka da suka fadi a zabe.

Shugabannin Amurka 10 kacal suka fadi a zaben tazarce a tarihi, da alamun Trump zai zama na 11 (Ga jerinsu)

Ga jerin tsaffin shugabannin Amurka da suka fadi a zaben tazarce:

1. John Adams (1797-1801)

2. John Quincy Adams (1825-1829)

3. Martin Van Buren (1837-1841)

4. Grover Cleveland (1885-1889)

5. Benjamin Harrison (1889-1893)

6. William Howard Taft (1909-1913)

7. Herbert Hoover (1929-1933)

8. Gerald Ford (1974-1977)

9. Jimmy Carter (1977-1981)

10. George H.W. Bush (1989-1993)

A yau, Talata, 13 ga Nuwamba, zaben shugaban kasan Amurka ke gudana: Yan Amurka sun fito kwansu da kwarkwatansu domin zaben shugaban da zai jagorancesu shekaru 4 masu zuwa.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


1 تعليقات

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN