Wasu yan fashi da makami guda hudu sun bakunci lahira bayan sun yi musanyar wutan bindigogi tsakaninsu da sojin Operatives of Operation Delta Safe, OPDS.
Rahotanni sun ce wadannan yan fashi da makami sun dade suna addabar al'umman Oyiore da ke karamar hukumar Ethiope ta gabas a jihar Delta.
Yan fashin dai sun buda wa sojin wuta da bindigogi ne bayan sun gansu, lamari da ya sa sojin suka mayar da martani da ya kai ga bindige yan fashin har lahira nan take.
Kwamandan sashe na 1 OPDS na sojin Najeriya Colonel Ahmed Sanni, Effurun, ya ce soji sun sami kiran ceton gaggawa daga al'umman Oyiore da karfe 10:04 na safe ranar 20 ga watan Nuwamba cewa yan fashi suna cikin garin.
Ya ce isar sojin ke da wuya sai yan fashi suka fara harbin soji da bindigoginsu. Ya ce soji sun mayar da martani sakamakon haka suka aika yan fashin lahira.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari