Na zama abin tausayi – Rahama Sadau

Fitacciyar jaruma Kannywood Rahama Sadau ta ce ta zama abin tausayi kan hotunan da ta saka da suka janyo cin mutuncin addininta.

Jarumar wadda tun a farko ta ce ta yi nadamar wallafa hotunan, ta shaida wa BBC cewa ta ji zafin yadda 'yan Kannywood suke maganganu kan lamarin, wanda ta ce ya faru ba tare da san ranta ba.

A ranar Litinin ne sunan Rahama Sadau ya fara waɗari a Twitter, inda aka ambaci sunan sau fiye da 10,000, bayan hotunan da ta tauraruwar ta saka suka ja hankalin masu bibiyarta da kuma masu amfani da Twitter musamman daga arewaci da kudancin Najeriya.

Hotunan jarumar sun haifar da mahawara tsakanin masu amfani da kafofin sadarwa, lamarin da har ya kai ga yin kalaman ɓatanci Annabi Muhammadu SAW.

Jarumar ta bayyana cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram sanye da hijabi, cikin kuka da murya mai rawa, tana neman a yafe mata.

A hirarta da BBC kuma ta ce duk wani mai hankali idan ya zauna ya kalli abin da ya faru zai gane cewa ta zama abin abin tausayi.

"Wani ya kamata ya yi tunanin shin ya Rahama take ji a matsayinta na musalma," in ji ta.

Ta ce da dare ta saka hotunan ta tafi ta yi bacci, ba tare da ta tsaya diba me ake cewa ba game da hotunan da ta wallafa.

"Sai da safe ina tashi na ga tsokaci dubu 10, ban san me ke faruwa ba. A haka wani ya turo min da sako na ɓatancin da aka yi. Ina ganin wannan na san cewa saka hoto ya koma wani abu"

Game da martani daga abokan sana'arta 'yan Kannywood, Rahama ta ce su ya kamata su fara ankarar da ita. "Amma kila waɗanda suke maganar sun riga ni gani amma ba za su iya kira na ba, gara su bari a yi ta magana akai"

Jarumar ta ce idan da tsokacin mutane ne kawai ba za ta damu ba. Amma ta ce yin ɓatanci ga Annabi SAW ya girgiza ta kuma shi ya sa ta ga ya dace ta fito ta bayar da hakuri saboda haushin da ta ji na cin mutunci addininta da aka yi.

"Duk wani musulmi dole ya ji haushi - shi ya sa na fito na ba jama'a hakuri kuma na nisanta kai na da kalaman da aka yi."

Jarumar ta ce wannan dalilin ne ya sa ta je ta ciro hoton gaba ɗaya. A cewarta idan da maganganun mutane ne kawai da suke yi game da hotunan ba za ta damu ba.

Source: BBC

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN