Mun yarda mun kasa taɓuka komai wa yaran Nigeria - Ministar kuɗi


Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta bukaci iyaye da su cusa wa yayansu akidar sanin martabobinsu a matsayin hanyar kare kasar daga durkushewa. Ministar ta yi kiran ne a ranar Asabar, a Kaduna a yayin wani taro na masu da hakimai 77, Shugabannin addinai da na gari daga kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna. 


“Mu na jan hankalin iyaye cewa mun gaza taɓuka komai wa yayanmu, duk martabobin da muke dasu a baya babu su a yanzu. “Ya kamata mu tunatar da kanmu cewa akwai bukatar yaranmu su kasance a mike sannan cewa wannan ta’asar da ke gudana, a kullu yaumin ba zai amfane su ba kuma ba zai amfani jihar da kasar ba,” in ji ta.

Ministar ta yi godiya bisa kokarin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi wajen kula da lamarin tsaro. Ahmed ta fada ma masu ruwa da tsakin cewa gwamnatin tarayya ta samar da wani shirin tallafawa matasa na naira biliyan 75. Ta ce an samar da shirin ne domin ba matasa a kasar damar habbaka kasuwancinsu da kuma dogaro da kai, jaridar Punch ta ruwaito.

Ministar ta yi bayanin cewa kudin zai tallafa wa matasan wajen sanin hazikancinsu da tunaninsu kan kasuwanci, zama masu amfani da kuma daukar wasu aiki. Da yake magana a wajen taron, ministan muhalli, Dr. Muhammad Mahmud, ya yi kira ga hadin kai wajen magance matsalolin tsaro a kasar.

Ya bukaci masu ruwa da tsaki a kan su tallafawa gwamnati wajen magance matsalolin tsaro da rashin aikin yi a kasar. A wani labari na daban, tsohon sanata Shehu Sani, ya ce wasu gwamnonin sun fi daraja indomie fiye da rayuwar jama'a.

Ya fadi hakan ne a matsayin martani a kan bin gida-gida da gwamnoni suka umarci jami'an tsaro don kwato kayan abincin da mutane suka sata daga ma'adanar gwamnati.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN